Kotu a Babban Birnin Tarayya ta Gamsu da Nuna Adawa da ba da Belin Abba Kyari
Wata kotu a babban birnin tarayya ta yi zama, ta duba yiwuwar ba da belin DCP Abba Kyari da ake zargi da harkallar kwayoyi.
Kotun ta ce ta duba batutuwa da dama da hukumar NDLEA ta gabatar, inda tace ta gamsu da nuna adawa da ba da belin nasa.
Ana tuhumar Abba Kyari ne tare da wasu jami’ai bayan da bidiyo ya yadu da ke nuna suna kokarin kulla harkallar kwayoyi.
Read Also:
Abuja- Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ki amincewa da bukatar neman belin da DCP Abba Kyari da mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, Sunday J. Ubua suka shigar.
Idan baku manta ba ana tuhumarsu da laifukan da suka shafi harkallar muggan kwayoyi tare da wasu mutane biyar, The Nation ta ruwaito.
Mai shari’a Emeka Nwite, a wani hukunci da ya yanke a safiyar yau Litinin, ya ce masu gabatar da kara sun gabatar da isassun hujjoji a gaban kotu domin nuna kin amincewa da belin manyan jami’an ‘yan sandan biyu.
A maimakon haka, Mai shari’a Nwite ya ba da damar ci gaba da sauraron karar.
Wasu hotunan da gidan talabijin na TVC ya yada ya nuna lokacin da Abba Kyari tare da sauran wadanda ake zargi ke zaune a bakin kotu.
Karin bayani na nan tafe…
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 10 hours 8 minutes 14 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 11 hours 49 minutes 39 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com