Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta Kame ‘Yan Kungiyar Asiri Guda 32 a Jihar Anambra
Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya reshen jihar Anambra ta sami nasarar kame mutum 32 da take zargi da ayyukan kungiyar Asiri a jihar.
Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan jihar DSP Toochukwu Ikenga, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar lahadi a garin Awka, inda yace dakarun sun sami nasarar bankado bindigu da wasu muggan makamai a hannun wadanda ake zargin.
Mista Ikenga yace samamen da suka kai maboyar ‘yan kungiyar Asirin na matsayin wani bangare na kokarin da hukumar ‘Yan Sandan ke yi na kawar da dukkan nau’in laifuka a jihar.
Ana dai zargin su ne da gudanar da ayyukan Ta’addanci, Fashi da Makami, mallakar makamai ba bisa Ka’ida ba, kamar yadda kakakin ya bayyana.
“A bisa wasu sahihan bayanai, da rundunar ‘Yan Sandan jihar ta samu a ranar 30 ga watan Maris ta sami nasarar kame wani Ozo Olie Ifeanyi, mai kimanin shekaru 43 a gidan sa dake kauyen Odoje a garin Onitsha, inda ta sami karamar bindiga guda daya da kuma Alburushi mai rai guda daya a cikin wata jaka.”
Read Also:
“sai dai yayi ikirarin cewa shi dan kungiyar Asiri ta Black AX ne, inda yake da kwarewa wajen yin kwace ga wadanda basu ji ba basu gani ba.”
“sannan a wannan rana hukumar ta sami nasarar kame wani da ake zargi, Ifeanyi Nwobu mai kimanin shekaru 49 a duniya dan asalin Enugu-Ukwu”.
“Rundunar ta sami nasarar kwato bindiga kirarar Beretta guda daya, da kuma harsashin guda daya daga hannun wanda ake zargin,” in ji shi.
Mista Ikenga ya kuma ce an kama wasu mutum 30 da ake zargi da aikata laifukan yaki daga shekaru 17 zuwa 44, da laifin karya dokar da gwamnatin jihar Anambra ta hana safara, da kuma karbar kudin haraji ba bisa ka’ida ba.
Yace an damke su ne a ranar 6 ga watan Afrilu a kusa da mahadar Tarzan, daura da kan titin Owerri da hanyar Upper Iweka, da mahadar Ochanja, sai kuma kan hanyar Awada da Head Bridge, da kuma mahadar kara da kan hanyar Atani.
Kakakin rundunar ya nanata kudurin kwamishin ‘yan sandan jihar Anambra, CP Echeng Echeng na kare lafiya da dukiyar al’ummar jihar daga duk wani laifi da rashin tsaro.
“Ba za mu taba yin kasa a gwuiwa ba wajen kare lafiya da dukiyoyin Al’umma, don haka muna kira ga mazauna yankin da su mayar da hankali wajen fallasa dukkanin ayyukan ta’addanci da bata gari ke aikatawa.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 12 hours 19 minutes 45 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 14 hours 1 minute 10 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com