Gidauniyar Malam Inuwa ta ba da Gudunmawar Mota ga Kungiyar Mata Masu Yaki da Cin Zarafin Mata da Kananan Yara
A ƙoƙarin da ta ke cigaba da yi wajen tallafawa rayuwar al’umma ta ɓangarori daban-daban, gidauniyar Malam Inuwa wacce mai girma shugaban hukumar bunƙasa fasahar sadarwar zamani ta ƙasa, (NITDA), Malam Kashif Inuwa Abdullahi, (CCIE), ya kafa ta ba da gudunmawar mota, (VR6) ga ƙungiyar mata masu yaƙi da cin zarafin mata da ƙananan yara ta ƙasar Haɗejia.
A lokacin da ya ke gabatar da jawabin miƙa mukullin motar, shugaban gidauniyar, Dakta Hussaini Yusuf Baban, ya bayyana cewa ba da gudunmawar ya biyo bayan buƙatar hakan ne da ƙungiyar ta gabatar gaba gare su, su ka kuma duba su ka tabbatar da cancantar hakan a gare su, inda daga bisani ya hore su da su yi amfani da motar ta duk hanyar da ta dace.
“Babu laifi dan kun yi amfani da motar wajen nemawa ƙungiyarku kuɗaɗen shiga domin gudanar da aikin ƙungiya, abin da ba a so shi ne amfani da ita wajen biyan buƙatar kai, amma babu wani aibu idan ku ka yi wani tsari wanda zai taimakawa ƙungiyar taku wajen samun abin dogaro da kai”. Cewar Dakta Hussaini Baban.
Read Also:
Ita ma a nata tsokacin jim kaɗan bayan karɓan mukullin motar, shugabar gidauniyar, Hajiya Fatima Kaila Nini Haɗejia, ta bayyana godiya da farin cikinta matuƙa bisa samun wannan gudunmawa inda kuma ta ƙara da bayyana cewa motar za ta taimaka matuƙa ainun wajen sauƙaƙa musu wahalhalun jigilar nemowa mata da ƙananan yara haƙƙoƙinsu a kotuna.
“Mun durƙusa a gun mutane masu yawa mun nemi gudunmawar wannan mota ba mu samu ba, amma cikin ikon Allah yau gashi wannan gidauniya ta tallafa mana da wannan mota wacce dama ita ce matsalarmu, mu na godiya da addu’ar fatan alkhairi a gare su”. Cewar Nini.
Haka zalika, gidauniyar ta Malam Inuwa ta kuma ƙara da ba wa Rabi’u Lauya tallafin mota ƙirar (Golf) domin dogaro da kai, inda shi ma ya bayyana farin cikinsa matuƙa da godiya ga Allah da wannan gidauniya tare da ba da tabbacin yin amfani da ita ta hanyar da ta dace.
“Na kasance direba wanda na ke tuƙa motar wani, yau Allah Ya azurta ni da tawa, ina godiya marar adadi ga Allah da waɗanda su ka ba ni, Allah Ya sa ta zama silar da ni ma zan iya ba wa wa wani zuwa gaba, na gode”. Inji Lauya.
An gudanar da wannan ƙwarya-ƙwaryar biki na miƙa waɗannan mukallan mota da motocin a gidan mai girma shugaban hukumar ta (NITDA), kana kuma jagoran gidauniyar, Malam Kashif Inuwa Abdullahi, (CCIE) a wannan rana.
Alhamis, 5 ga watan Afrelu, 2022.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 10 hours 44 minutes 49 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 12 hours 26 minutes 14 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com