Home Labarai Buhari ya Bukaci ASUU Ta Kawo Karshen Yajin Aikin Da Take Yi

Buhari ya Bukaci ASUU Ta Kawo Karshen Yajin Aikin Da Take Yi

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya bukaci kungiyar malaman Jami’an ta ASUU, da ta kawo karshen yajin aikin da take yi.

Buhari ya yi wannan kira ne wajen biki murnar zagayowar ranar samun albakatun kasa gami da bada lambar yabo da aka gudanar a fadar shugaban dake birnin tarayya Abuja

Buhari ya bukaci kungiyar data janye matakin data dauka na yajin aikin, la’akari da halin da daliban Jami’oin kasar ke ciki sakamakon yajin aikin da suka tsunduma.

Ya kuma bukaci kungiyar Dalibai ta kasa NANs ta kara hakuri, kasancewa gwamnati na kokarin shawo kan matsalar.

Buhari yace ko a ranar daya ga watan Fabreru ya umarci shugaban Ma’aikatan Fadar gwamnatin tarayya Farfesa Ibrahim Gambari, Ministan Kwadago da Ayyuka Chris Ngige, da kuma Ministan Ilimi Adamu Adamu, su san mai yiwuwa wajen ganin an magance matsalar yajin aikin

A ranar litinin din wannan makon kungiyar Malaman Jami’ar ta ASUU ta sanar da kara wa’adin yajin aikin da take zuwa watannin Uku (3).

Kungiyar dai na bukatar wasu makudan kudade domin farfado da jami’oin Gwamnati, gami da samar da tsarin biyan albashi na (UTAS) da kuma wasu bukatu da take nema a wajen gwamnatin tarayya Nijeriyar.

Sauran bukatan sun hadar da cika musu alkawarin da gwamantin tarayyar Nijeriyar tayi a cikin wata takardar da aka sanya hannu a alkawarin kungiyar da Gwamantin tarayya na shekarar 2019, tare da nuna rashin gamsuwa da tsarin biyan Albashin bai day ana IPPIS.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
HOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna YusufYadda Hon. Hudu Kanje Ya Sake Fasalin Jagorancin Cigaban Kasa Daga Mika'il Ja'afarƳan Sanda Sun Kama Mutane 300 a Farmakin Wuraren da Ake Aikata Laifuka a FCT Sun Kwace Wukake, Bindigar Wasa, da WiwiZakari Mohammed: Dole Kwara ta Cika Kwarewarta – Dan Takarar ADC ya Nemi Muhawara a BayyaneWSCIJ ta Yaba wa PRNigeria Kan Ci Gaba da Tallafawa Matasa Wajen Sadarwa Bayan Karewar Tallafi
X whatsapp