Home Labarai Rundunar Sojojin Ruwan Nijeriya ta Nemi Hadin Gwuiwar PRNigeria

Rundunar Sojojin Ruwan Nijeriya ta Nemi Hadin Gwuiwar PRNigeria

Babban hafsan sojin ruwa CNS, Vice Admiral Awwal Zubairu Gambo, ya bayyana farin cikinsa game da yadda PRNigeria ke wallafa labaran da ya shafi sojoji da fannin tsaro ba tare da nuna son rai ba.

Ya bayyana hakan ne ta bakin kakakin rundunar sojojin Ruwan Commodore Adetun Ayo-Vaughan, wanda ya jagoran tawagar jami’an rundunar wata ziyarar kafa da kafa zuwa hedikwatar jaridar dake Birnin tarayya Abuja.

A cewar, PRNigeria zata cigaba da kasancewa kamfanin dillancin labarai na daya kuma taka tabbatar da wallafa da sahihin labari kan ayyukan sojoji da sauran jami’an tsaro.

Yace: PRNigeria ta tabbatarwa da kanta tsayuwa kan gwadaben wallafa labaran gaskiya da gaskiya kan lamurran tsaro musamman sojojin Nijeriya.

Ya kara da cewa sojojin Nijeriya sun yaba da ayyukan PRNigeria. Don haka kakakin rundunar yace akwai bukatar a bunkasa alakar dake akwai tsakanin rundunar da Jaridar ta PRNigeria.

Da yake karbar bakin, babban Editan rukunin jaridun dake karkashin kamfanin Image Merchants Promotion (IMPR) Limited dake mallakin PRNigeria Mal. Yusha’u Shuaib, ya yaba kakakin rundunar sojin Ruwan bisa wannan ziyara.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
HOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna YusufYadda Hon. Hudu Kanje Ya Sake Fasalin Jagorancin Cigaban Kasa Daga Mika'il Ja'afarƳan Sanda Sun Kama Mutane 300 a Farmakin Wuraren da Ake Aikata Laifuka a FCT Sun Kwace Wukake, Bindigar Wasa, da WiwiZakari Mohammed: Dole Kwara ta Cika Kwarewarta – Dan Takarar ADC ya Nemi Muhawara a BayyaneWSCIJ ta Yaba wa PRNigeria Kan Ci Gaba da Tallafawa Matasa Wajen Sadarwa Bayan Karewar Tallafi
X whatsapp