Home Labarai Kwamishin ‘Yan Sandan jihar Zamfara na ziyarar tabbatar da Zaman lafiya a...

Kwamishin ‘Yan Sandan jihar Zamfara na ziyarar tabbatar da Zaman lafiya a Jihar

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara, CP Kolo Yusuf PSC, ya ziyarci sansanin wucin gadi na horas da masu hidimar kasa dake makarantar sakandiren ta kimiyya dake Gusau
Wannan na kunshe ta cikin wata sanarwa mai dauke da kwanan watan 11 ga watan Nuwamba 2022 da kakakin rundunar yan sandan jihar SP Muhammad Shehu ANIPR ya aikowa da PRNigeria.

Inda sanarwa tace ziyarar na wani bangare na tabbatar da zaman lafiya a jihar dake arewa maso yammacin Nijeriya.

Kwamishinan ya kai ziyarar ne domin ingantawa gami da karfafa tsare-tsaren tsaron a sansanin da nufin tabbatar da tsare dukkan masu hidimar kasa dake jihar baki daya.
A yayin jawabin sa ga masu hidimar kasar kwamishinan ‘yan sanda ya basu tabbatacin cewa ‘yan sanda zasu jajirce wajen kare rayukan su a sansanin da kuma wurare.

Daga bisani ya bukace su dasu kasance masu lura gami da kai rahoton ga ‘yan sanda da sauran hukumin tsaro kan dukkan abinda ya shige musu duhu domin daukar matakan gaggawa.

ko dai a cikin wannan mako an gano kwamishinan na wata ziyarar zuwa Jami’ar gwamnatin tarayya dake Gusau da kwalejin Ilimi da kere-kere ta tarayya, gami da Makarantar sakandire da “yan sanda dake jihar.

Jihar Zamfara dai na guda cikin jihohin dake Arewacin Nijeriya dake fama da matsalolin rashin tsaro sakamakon ‘yan bindiga masu satar mutane domin karbar kudin fansa da wasu matsaloli da ke da alaka da rashin tsaro a jihar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
HOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna YusufYadda Hon. Hudu Kanje Ya Sake Fasalin Jagorancin Cigaban Kasa Daga Mika'il Ja'afarƳan Sanda Sun Kama Mutane 300 a Farmakin Wuraren da Ake Aikata Laifuka a FCT Sun Kwace Wukake, Bindigar Wasa, da WiwiZakari Mohammed: Dole Kwara ta Cika Kwarewarta – Dan Takarar ADC ya Nemi Muhawara a BayyaneWSCIJ ta Yaba wa PRNigeria Kan Ci Gaba da Tallafawa Matasa Wajen Sadarwa Bayan Karewar Tallafi
X whatsapp