Shugaban Najeriya Muhammadu ya Buhari ya bi sahun shugabannin ƙasashen duniya wajen miƙa saƙon ta’aziyyarsa kan rasuwar fitaccen ɗan ƙwallon duniya Edson Arantes do Nascimento wanda aka fi sani da Pele.
A wata sanarwa da mataimaki na musamman ga shugaban ƙasar kan kafofin yaɗa labarai Malam Garba shehu ya fitar, shugaba Buhari ya bayyana ɗan wasan da cewa mutum ne ”mai kirki da ƙanƙan da-kai, duk da cewa shi babban ɗan wasa ne”.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
”Pele ya gina kyakkyawar alaƙa tsakanin ƙasashe, da ƙabilu da ma addinai, haƙiƙa duniya ba za ta manta da shi ba”, kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Tsohon gwarzon ɗan wasan duniyar ya mutu ne ranar alhamsi bayan ya sha fama da rashin lafiya.
Ya lashe kofin duniya uku tare da zura ƙwallaye sama da 1,281, ya zama zaƙaƙurin ɗan wasan duniya.












