Kwamandan Rindunar dake lura da yankin Abuja, Commodore Abdulrahman Muhammed, inda ya yabawa manyan Jami’an rundunar bisa kyawawan hali gami da kwarewa da yadda suke gudanar da ayyukan su cikin sadaukarwa.
Kwamandan ya bayyana hakan ne a wani biki mai lakabin Naval Unit Abuja Social Activities (NUASA 2022) wanda ke nuna an kawo karshen shekarar 2022.
Ya kuma bukace su dasu kara kaimi wajen sake firo da kimar rundunar ta sojin Ruwan Nijeriya.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Babban shugaban sashen Mulki na Shalkwatar rundunar Rear Admiral Barabutemegha Jason Gbassa wanda ya sami wakilcin Rear Admiral Kennedy Obi Egbuchulam, wanda shima ya bukaci jami’an dasu kasance masu sadaukar da kai, Da’a da kuma nuna gogewar aikin na soja ta hanyar kare lafiya da dokiyoyin Al’umma.
Yace “ina matukar yaba muku bisa rawar da kuka taka wajen samun nasarar rundunar Sojojin Ruwan Nijeriya. wannan ya samar da yanayi mai ga Al’ummar birnin Abuja masu kaunar zaman Lafiya domin gudanar da bikin Kirsimeti da sabuwar shekara.
Bikin na Naval Unit Abuja Social Activities (NUASA 2022) ya sami halartar iyaye, yara inda aka gudanar gasa kala-kala, wasan barkwanci, tambayoyi da amsa ga yara domin kara armashin taron.












