Babban Hafsan sojojin Nijeriya Gen. Lucky Irabor yace za’a mayar da Tubabbun ‘yan ta’adda 613 da aka dora bisa tafarki mai kyau zuwa gwamnonin jihohin su don su koma cikin Al’umma.
Irabor ya bayyana hakan ne a wani taron masu ruwa da tsaki da dakarun Operation Safe Corridor (OPSC) karo na 5 ranar Alhamis a birnin Abuja.
Irobor wanda ya sami wakilcin Manjo Janar
Adeyemi Yekini daje lura da sashen horaswa da sumame na rundunar yace Irabor yace Tubabbun 613 na bisa kulawar gyaran hali karkashin (OPSC).
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Yace taron ya tattauna kan gyarawa gami da wayar da kan su wanda a turance aka kira da Deradicalization, Rehabilitation and Reintegration wato (DRR) kafin mika su ga Gwamnatocin jihohin su.
Irabor yace rundunar ta OPSC yace shugaban kasa Muhammadu Buhari ne samar da ita a watan satumbar 2015, a wani bangare na bada dama ga ‘yan Ta’adda dimin su ajje makamansu.
Ya kara da cewa shirin ya kunshi hukumomi da cibiyoyin jin kai 17 dake samun tallafi daga suka hadarwanda akayu amfani su tallafi daga kungiyoyin gida dana ketare.
Irabor yace nasarar Rundunar ta OPSC sun cigaba da yaduwa gani samun nasara, abinda yaja hankulan kasashe da masu nazari domin gudanar da bincike.
Irabu ya bukaci gwamnonin dake karbar tubabbun da su basu tallafi don tsamo rayuwar su daga kakanakayi.
PRNigeria












