Kungiyar dillalan man fetur ta kasa ta janye umarnin da ta baiwa ‘ya’yan kungiyar na rufe gidajen mai a duk fadin Nigeria.
Sanarwar janyewar na dauke ne cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar na kasa Alhaji Muhammad kuluwa ya sanyawa hannu kuma aka rabawa manema labarai.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Sanarwar ta ce an janye umarnin ne sakamakon cigaba da tattaunawa da kungiyar ta ke yi da hukumomin da abun ya shafa ,domin magance matsalolin da yan kungiyar suke fuskanta.
Idan za’a iya tunawa PRNigeria ta rawaito Kungiyar ta IPMAN ta baiwa ‘ya’yan ta umarnin rufe gidajen mai a fadin Nigeria, Inda Kuma kasa da sa’a guda ta janye umarnin.
PRNigeria hausa











