Rundunar sojin ruwa ta Najeriya ta kuɓutar da mutum 18 da aka yi safarsu a unguwar Rijiyar Lemu da ke ƙaramar hukumar Ungogo a jihar Kano da ke arewacin Najeriya
Wannan na kunshe ta cikin wata sanarwa da daraktar yada labaran ta AO AYO-VAUGHAN Commodore ya fitar, wadda tace ta kama mutum biyu da take zargi da hannu wajen safarar mutanen.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Rundunar ta ce ta samu nasarar kuɓutar da mutanen ne bayan da wani jami’insu ya ankarar da su kasancewa ‘yar uwarsa na daga cikin mutanen da aka yi safar tasu.
Sojojin ruwan sun ce sun miƙa mutanen tare da waɗanda ake zargin hannun hukumar da ke yaƙi da safarar bil-adama ta ƙasar domin ɗaukar mataki.












