Shugaba Muhammadu Buhari ya jajanta wa waɗanda gobara ta kona wa shaguna a kasuwa sayar da kayan mota da ke jihar Legas a kudancin Nijeriya.
wannan na kunshe ta cikin wata sanarwa da mataimaki na musamman kan harkokin yaɗa labarai ga shugaban Malam Garba Shehu ya fitar, ta ce shugaban ya nuna alhini kan abin da ya faru da ‘yan kasuwar da kuma iyalansu, inda ya nuna takaici kan irin asarar dukiya ta miliyoyin naira da aka yi a kasuwar.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Ya yi kira ga hukumomi a jihar da su tabbatar sun ɗauki matakin kare afkuwar hakan nan gaba, inda ya godewa hukumar kashe gobara ta jihar saboda kai agajin gaggawa lokacin da lamarin ya faru.
Buhari ya kuma miƙa ta’aziyya ga iyalan wani mai gadi mai shekara 65 da ya rasu a sanadiyyar gobarar.
PRNigeria Hausa












