Rahotanni daga Kamaru na bayyana cewa Jagoran jam’iyyar adawar kasar ta SDF John Fru Ndi ya mutu a daren litinin ya na da shekaru 81 bayan fama da jinya.
Jagoran adawar shi ne dan siyasa mafi dadewa da ya ci gaba da zama a jam’iyyar adawa tun zuwan siyasar jam’iyyu da dama a kasar.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
John wanda ya yi fama da doguwar jinya shi ne dan siyasa daya tilo da ya shafe tsawon lokaci ya na watsi da tayin shugaban kasar Paul Biya wanda ya nemi ya shiga cikin gwamnatin don tafiya tare.
John Fru Ndi ya shafe tsawon shekaru ya na caccakar salon kamun ludayin gwamnatin Paul Biya shugaban da ya shafe shekaru 38 ya na mulkar kasar ta gabashin Afrika.
Zuwa yanzu dai ba a sanar da lokacin gudanar da jana’izar jagoran adawar mai shekaru 81 ba, sai dai tuni ‘yan kasar suka fara makokinsa.
PRNigeria hausa












