Yan majalisar dattawa da suka Fito daga Yankin arewacin Nijeriya sun kalubalanci yunkurin kungiyar raya tattalin arzikin Afirka ta Yamma, ECOWAS, na amfani da karfin soji kan sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar.
Sun bayyana haka ne a yayin da shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya rubuta wasika ga majalisar dattawan kasar yana neman amincewarta don daukar matakin soji kan sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar.
Shugaban ya kuma nemi izinin daukar wasu matakai ciki har da katse wutar lantarkin da Nijeriya ke bai wa Nijar.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Mai Magana Da Yawun Kungiyar Kuma Sanatan Kano ta kudu Sanata Abdurrahman kawu sumaila yace Baza su amince da duk wani Mataki na yaki da Nijeriya da Jamhuriyar Niger ba, Saboda doguwar alakar Dake tsakanin Yankin arewacin Nigeria da ita.
Shugaban majalisar dattawan kasar Godswill Akpabio ne ya karanta wasikar da Shugaba Tinubu ya rubuta wa majalisar a zaman da ta yi ranar Juma’a.
Ya aike da wasikar ne bayan rashin nasarar tawagar da kungiyar ECOWAS ta tura Nijar don tattaunawa da sojojin kasar don mayar da Shugaba Mohamed Bazoum kan karagar mulki.
Tuni dai sojojin ECOWAS suka fara nuna bukatar su na afkawa dakarun sojin na Nijar domin dawo da Kasar turbar Damukradiyya.
PRNigeria Nijeriya












