Rahotanni daga nijeriya na tabbatar da yadda akalla fursunoni 118 ne suka tsere daga gidan yarin Suleja da ke jihar Naija mai maƙwabtaka da birnin Abuja, sakamakon ruwan sama mai kama da bakin ƙwarya da ya ruguza wani ɓangaren ginin gidan ranar Laraba.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Mai magana da yawun hukumar gyaran hali ta birnin Tarayya, Adamu Duza, a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis ya ce “sakamakon ruwa kamar da baƙin ƙwarya da ya kwashe awa 24 yana zuba ya lalata wasu sassan gidan yarin inda fursunoni 118 suka tsere.”
To sai dai wani jami’in gidan yarin da ya gana da manema labarai ya bayyana cewa kawo yanzu an samu damar kama fursunonin 10 daga cikin 118 ɗin da suka tsere, inda kuma suke ci gaba da baza komar neman mutum 108.
PRNigeria hausa












