Home General Ambaliya ta kashe mutum 195 a Najeriya – NEMA

Ambaliya ta kashe mutum 195 a Najeriya – NEMA

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya (NEMA) ta ce ambaliyar ruwa ta yi sanadiyar mutuwar aƙalla mutum 195 a jihohi 15 na ƙasar a shekarar 2024.

Hukumar ta kuma ce ambaliyar ta raba ƙarin wasu fiye da mutum 208,000 da muhallansu a cikin jihohi 28.

A cikin rahoton da ta fitar kan ƙididdigar ɓarnar da ambaliya ta yi a Najeriya a cikin 2024, NEMA ta ce fiye da kadada 107,000 da gidaje 80,000 ne ambaliyar ta lalata a bana.

Babbar daraktar hukumar NEMA, Hajiya Zubaida Umar, ta shaida wa manema labarai cewa: ‘‘Hasashen yanayi da muka samu daga cibiyar aikin gaggawa da muka kafa a cikin watan Yuli, ya nuna cewa ƙananan hukumomi 140 wannan ambaliya ta shafa, a cikin jihohi 28’’

‘‘Sannan mutum 548,494 ne ambaliyar ta shafa, kuma a cikinsu aƙalla mutum 2,000 ne suka ji rauni sakamakon ambaliyar’’

Hajiya Zubaida Umar ta ƙara da cewa jihohin da ambaliyar ta fi shafa sun haɗa da Bauchi da Zamfara da Sokoto da kuma Jigawa.

‘‘Jihar Bauchi ce ta ɗaya, amma a Jigawa aka fi samun asarar rayuka, amma a Bauchi da Zamfara ne aka fi tafka asarar da ta shafi sauran abubuwa’’

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa'adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDPAIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da ZamfaraSojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta'addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a SokotoCOAS Shaibu ya yi Kira da a Haɗa Kai Yayin da Sojoji Ke Faɗaɗa Zuwa Rukunoni 12Najeriya ta Shirya Horarwa ta Yankuna Kan Gano da Bin Diddigin Ƙananan MakamaiSojoji Sun Kai Harin Sama da ya Hallaka Ƴan ISWAP Sama da 40, ya Lalata Motoci a BornoAmurka ta Zargi Najeriya da Daukar Yara Sojoji, Masana'antun Jarirai da Fataucin MutaneHaɗaka DMI da TMS a London ta Tsara Sabuwar Hanyar Goyon Bayan Tinubu Zuwa 2027Yushau Shuaib @57: Bikin Jagora Wanda ya Buɗe Kofofi da Canza Rayuka Daga Hafsat Ibrahim Yusha'u Shuaib @57: Barka da zagayowar Ranar Haihuwa ga Jagoran Mazaje, Mutumin da Ya Bani Dama Daga Ozumi AbdulHarin Jirgin Sama a Filin Jirgin Saudiyya ya yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 12, Raunata 309Trump ya yi Kira ga Sabon Shugaban Ukraine, ya Zargi Zelensky da Kin Amincewa da Yarjejeniyar Zaman LafiyaAFRI-CIRD ta yi Kira ga Gwamnatoci su Kara Kudin Ilimin Ƴa'ya MataAmnesty International ta yi Allah Wadai da Toshe Taron 'Dole Tinubu Ya Tafi' da Ƴan Sanda Suka yi a KanoTMG vs TMS: Matsalar Sadarwa Kan Makomar Tinubu Daga Yushau A. Shuiba 
X whatsapp