Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta yi hasashen cewa mamakon ruwan sama da za a yi kwana biyar ana yi, zai janyo ambaliyar ruwa a wurare 123 na jihohi 21 na ƙasar.
Rahoton ya bayyana jihohin Benue da Kogi da Anambra da Delta da Rivers da Imo da Bayelsa a matsayin jihohin da iftila’in zai fi ƙamari.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Jaridar Punch a Najeriya ta ruwaito cewa wani rahoto da hukumar kare muhalli ta fitar ya yi kira ga mazauna waɗanann jihohi riƙa sanya idanu tare da lura da al’amura.
Gwamnatin ta kuma bayyana cewa yankuna 123 ne za su iya fuskantar ambaliyar, wadda ake hasashen zai faru tsakanin 4 ga Satumba zuwa 8 ga Satumba.











