Home General Gwamnatin Najeriya ta ce ba ta da hannu wajen ƙarin kuɗin fetur...

Gwamnatin Najeriya ta ce ba ta da hannu wajen ƙarin kuɗin fetur a ƙasar.

Hoton Tinubu

Ministan yaɗa labaran Najeriya, Mohammed Idris ya ce gwamnatin tarayya ba ta da hannu wajen ƙarin kuɗin mai na baya-bayan nan.

“Dalilan da suka kawo wannan ƙarin farashin sun haɗa da rikicin gabas ta tsakiya, saboda ya haifar da tashin farashin mai a kasuwannin duniya.”

Ministan ya yi kira ga ƴan Najeriya da su ci gaba da ba NNPCL da gwamnatin haɗin kai, “Gwamnati za ta yi amfani da kuɗin tallafin da aka cire wajen inganta fannin lafiya da ilimi, tsaro.”

Kamfanin mai na Najeriya NNPCL ya yi ƙarin kuɗin fetur a ranar Laraba, inda farashin ya tashi daga naira 897 zuwa 1,030 kowace lita a Abuja, yayin da a jihar Lagos ya tashi daga naira 855 zuwa 998.

A jihohin arewa maso gabas, man ya koma naira 1,070 a yankin kudu maso yamma, naira 1,025 jihohin kudu maso gabas ya kai naira 1,045.

Matakin ya janyo cece-kuce a tsakanin ƴan Najeriya, inda suke ci gaba da neman shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi wani kan tashin farashin man.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
HOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna YusufYadda Hon. Hudu Kanje Ya Sake Fasalin Jagorancin Cigaban Kasa Daga Mika'il Ja'afarƳan Sanda Sun Kama Mutane 300 a Farmakin Wuraren da Ake Aikata Laifuka a FCT Sun Kwace Wukake, Bindigar Wasa, da WiwiZakari Mohammed: Dole Kwara ta Cika Kwarewarta – Dan Takarar ADC ya Nemi Muhawara a BayyaneWSCIJ ta Yaba wa PRNigeria Kan Ci Gaba da Tallafawa Matasa Wajen Sadarwa Bayan Karewar Tallafi
X whatsapp