Majalisar dattijan Najeriya ta sanar da jingine tattaunawa kan ƙudurin sauye-sauye ga dokar haraji ta ƙasar, wadda shugaban ƙasar Bola Tinubu ya gabatar mata.
Majalisar ta ɗauki wannan matsaya ce a yau Laraba a lokacin muhawararta a zauren majalisar da ke Abuja.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Hakan na zuwa ne kwana ɗaya bayan da gwamnatin ƙasar ta umarci ma’aikatar shari’a ta ƙasar ta yi aiki tare da Majalisar Dokokin domin samun masalaha kan wasu ɓangarori na dokar da ake taƙaddama a kai.
Tattaunawa kan ƙudurin ya janyo zazzafar muhawara a faɗin Najeriya, yayin da wasu ɓangarorin ƙasar suka yi zargin cewa an cusa wasu abubuwa da za su cutar da wasu yankunan ƙasar.
A yanzu Majalisar ta umarci kwamitin da ta miƙa wa ƙudurin da ya jingine duk wani nazari a kansa, yayin da aka kafa wani kwamiti wanda zai yi aiki tare da ma’aikatar shari’a ta ƙasar domin duba ɓangarorin ƙudurin da ake taƙaddama a kai.












