Home General Gwamnatin jihar Zamfara ta haramta taron siyasa a jihar

Gwamnatin jihar Zamfara ta haramta taron siyasa a jihar

Gwamnatin jihar Zamfara ta hana gudanar da tarukan siyasa karkashin kowacce jam’iyya a duk fadin jihar, har sai yadda hali ya yi.

Gwamnatin ta ce ta dauki matakin ne domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Matakin dai ya biyo bayan aukuwar wasu tashe-tashen hankula masu nasaba da siyasa, kuma jam’iyyar adawa ta APC a jihar ta koka cewa an kai jami’anta hari.

Mustafa Jafaru Kaura, shi ne babban mataimaki na musamman ga gwamnan jihar ta Zamfara, kan kafafen watsa labarai da al’amuran jama’a, ya shaida wa BBC cewa, an dauki wannan mataki ne sakamakon wata hatsaniyar siyasa da ta auku a yankin karamar hukumar Maru.

Ya ce, “Daga yanzu an haramta duk wani taro ko gangami da zai iya tayar da hankalin wasu har su ga kamar ba a yi musu daidai ba a yayin da gwamnatin jihar ke jimamin abin da ya faru a karamar hukumar Mulkin Maru inda aka rasa rayuka da kona dukiya mai yawa.”

Ya kara da cewa wannan haramci na wuci gadi ne bana din-din-din ba.

Mustafa Jafaru Kaura, ya ce,” Maslahar al’umma gwamnati ta duba shi ya sa ta dauki wannan mataki ba wai an yi haka don a tozarta wasu ba ne.”

Babban mataimaki na musamman ga gwamnan jihar ta Zamfara kan kafafen watsa labarai da al’amuran jama’a, ya kara da cewa wannan haramci da gwamnati ta sa kan taruka da sauran wasu hidimomi na siyasa a jihar, ya fara aiki nan take tun daga ranar Asabar, kuma gwamnatin ta umarci jami’an tsaro da su dauki tsaurara matakai kan duk wani dan siyasa ko gungun ‘yan siyasa da ya yi kunnen kashi da wannan gargadi a illahirin jihar, ba tare da la’akari da bambancin siyasa ba.

To sai kuma reshen jam’iyyar APC mai adawa a jihar, ya soki wannan mataki in da ya ce za zata sabu ba.

Mai magana da yawun reshen jam’iyyar ta APC a Zamfarar, Malam Yusuf Idris Gusau, ya ce ace an hana taron siyasa ai abin dariya ne, tun da ba gangamin yakin neman zabe aka ce za a yi ba.

Ya ce,”Babu wata doka da ta bayar da dama ace na hana taron siyasa, kuma ai ba taron siyasa ya hana ba, taron da aka yi na jam’iyyar APC a Zamfara ranar Asabar ne ya bawa gwamnati mai ci tsoro, shi yasa gwamnatin ta fitar da wannan sanarwa.”

“Mu fa gwamnati bata isa ta hanamu taron siyasa ba domin jam’iyyarmu jam’iyya ce mai rijista a kasa.”

Malam Yusuf Idris Gusau,ya ce,”Mu mutanen jam’iyyarmu mutane ne masu biyayya ga dokokin kasa da kuma tabbatar da cewa bamu kawo wani tashin hankali a jiha ba.”

Bisa ga dukkan alamu dai an sa zare tsakanin bangaren gwamnatin jam’iyyar PDP mai mulki da jam’iyyar adawa ta APC a jihar ta Zamfara.

Kuma masu sharhi kan al’amura siyasa na ganin wannan lamarin yana bukatar kulawar gaggawa daga dattawa da sauran masu fada-a-ji na bangarorin biyu, da kuma jami’an tsaro a daya bangaren tun kafin cibi ya zama kari.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa'adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDPAIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da ZamfaraSojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta'addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a SokotoCOAS Shaibu ya yi Kira da a Haɗa Kai Yayin da Sojoji Ke Faɗaɗa Zuwa Rukunoni 12Najeriya ta Shirya Horarwa ta Yankuna Kan Gano da Bin Diddigin Ƙananan MakamaiSojoji Sun Kai Harin Sama da ya Hallaka Ƴan ISWAP Sama da 40, ya Lalata Motoci a BornoAmurka ta Zargi Najeriya da Daukar Yara Sojoji, Masana'antun Jarirai da Fataucin MutaneHaɗaka DMI da TMS a London ta Tsara Sabuwar Hanyar Goyon Bayan Tinubu Zuwa 2027Yushau Shuaib @57: Bikin Jagora Wanda ya Buɗe Kofofi da Canza Rayuka Daga Hafsat Ibrahim Yusha'u Shuaib @57: Barka da zagayowar Ranar Haihuwa ga Jagoran Mazaje, Mutumin da Ya Bani Dama Daga Ozumi AbdulHarin Jirgin Sama a Filin Jirgin Saudiyya ya yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 12, Raunata 309Trump ya yi Kira ga Sabon Shugaban Ukraine, ya Zargi Zelensky da Kin Amincewa da Yarjejeniyar Zaman LafiyaAFRI-CIRD ta yi Kira ga Gwamnatoci su Kara Kudin Ilimin Ƴa'ya MataAmnesty International ta yi Allah Wadai da Toshe Taron 'Dole Tinubu Ya Tafi' da Ƴan Sanda Suka yi a KanoTMG vs TMS: Matsalar Sadarwa Kan Makomar Tinubu Daga Yushau A. Shuiba 
X whatsapp