Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yaba wa tsohon gamnan jihar Kaduna Mallam Nasir El-Rufai kan gudunmowar da ya bayar a fannin dimoƙraɗiyyar ƙasar.
Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, domin taya El-Rufai munar cika shekara 65 a duniya, Tinubu ya bayyana tsohon gwamnan na Kaduna da jagora, manazarci kuma ɗan siyasa.
”Irin gudunmowar da ya bayar wajen hidimta wa ƙasa da zama abin koyi ga ƴan baya, babban abin yabawa ne”, a cewar sanarwar.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Shugaba Tinubu ya kuma yaba wa rawar da El-Rufai ya taka wajen kafuwar jam’iyyar APC, da kuma irin gudunmowar da ya bayar wajen nasarorin jam’iyyar a zaɓukan ƙasar uku da suka gabata, 2015 da 2019 da kuam 2023.
A shekarar 2015 ne aka zaɓi Mallam Nasir El-Rufai a matsayin gwamnan jihar Kaduna, inda ya yi wa’adin mulki biyu.
Bayan rantsar da Shugaba Tinubu a 2023 ya sanya sunan El-Rufai cikin jerin mutanen da yake son bai wa muƙaman ministoci, sai dai tsohon gwamnan bai tallake tantancewar majalisar dattawan ƙasar ba, lamarin da ya sa bai samu muƙamin ba.
Daga nan ne kuma dangantaka ta fara tsami tsakaninsa da Tinubu, inda a baya-bayan ya riƙa fitowa fili yana sukar manufofin gwamnatin.












