Bincike: Shin da gaske ne an fuskanci yana sanyi mai tsananin gaski a garin Jos wanda har kankara ke zuba?

IKIRARI: wani faifen Bidiyo da aka yada a kafafen sada zumunta na zamani, wanda ke nuna wata mata da wani abu mai kama da dusar kankara ya ke kewaye da ita bawan zubar ta, bidiyon ya yi ikirarin cewa garin Jos ne, babban birnin jihar Filato, dake tarayya Nijeriya.

A jikin bindiyon an rubuta “Dusar Kankara a Jos, Jihar Filato. Yanayin sanyi (winter) a Nijeriya? ABIN MAMAKI! Sauyin yanayi gaskiya ne,” ana lakanta canjin yanayin yana aukuwa saboda sauyin yanayi.

A bidiyon, an ga matar mamakin yanayin na “dusar kankara”, tana kuma daga abun da ya yi kama da kankarar ga wadanda suka zagaye ta suna kallo, cikin su har da matuka Babura da suak taru a wajen.

Tabbatar da sahihanci: domin  tabbatar da sahihancin abin da ake ikirari akai PRNigeria ta bi diddigin bidiyon na asali, wanda aka yada shi a wajen 21 ga watan Afrilun 2025.

Dukka dai haka, PRNigeria ta bincika rahoton hasashen yanayi a birnin Jos da ga watan Afrilun 21 zawa 29 ga watan Afrilun 2025. Hasashen ya bayyana karara cewa yanayi ya kasance gajimare jifa-jifa bisa ga ma’aunin Celcious 240C zuwa 300C. babu wani rahoton da ya nuna akwai yanayin zubar dusar kankara a dukkan yanayin.

An sake fadada bincike da suka hadar da yin amfani da hanyar binciken sahihancin bidiyo, wanda kuma ya tabbatar da an wallafa bidiyon ne  a kasar Kamaru. An wallafa shi ne a shafin facebook na NexDim Empire, shafin da ke yada abubuwan da suka shafi nishadantar a kasar wanda ke da mabiya sama da dubu 234.

Wadanda ke bayyana ra’ayin su karkashin bidiyon wanda aka tabbatar da ‘yan asalin kamaru ne wadanda ke korafin cewa dusar kankara ta lalata musu amfanin gona, har wani da ake kira da Terry Mcberi yak e cewa:

“dusar kankarar da ke zuba ta lalata mana amfanin gona amma mutane suna farin ciki, dan kankanin lokaci ya rage sai su ce basa jin dadin lokacin noma.

Wasu zababbun kalmomi da PRNigeria ta yi amfani da su sa ta tabbatar da yankin a kasar kamaru yake da ake kira da Aba Banki Tungoh wanda a arewa maso yammacin kasar yake, yankin da suke amfani da harshen Ingilishi.

Tarihin Zubar Dusar Kankara

Akwai karancin zubar dusar kankara sosai a yankin dake da yanayin zafi, sun taba samun rahoton samun zubar dusar kankarar kadan. Wanda an samu a a watan Disambar shekarar 1991, yayin da dusar kankarar ta zuba a wasu yankunan.

Kammalawa: binciken da PRNigeria ta gano wanda asalinsa ya fito ne da kasar Kamaru a yankin Aba Banki Tungoh, ba a garin Jos da ke Nijeriya ba.

Ikirarin da ake kan cewa an sami zubar dusar kankara a garin Jos ba gaskiya bane.

HukunciPRNigeria ta yanke hukunci kan wannan ikirari da ke cewa an sami zubar dusar kankarar  a garin Jos, saboda sauyon yanayin labara ne na Karya

PRNigeria

 

 

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1462 days 8 hours 44 minutes 21 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1444 days 10 hours 25 minutes 46 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com