Home Labarai Gwamnatin tarayya ta dauki matakan dakile sake yajin aikin ASUU a Nijeriya

Gwamnatin tarayya ta dauki matakan dakile sake yajin aikin ASUU a Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Jaddada Aniyarta na Kawo Karshen Matsalolin Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU)

Ministan  ilimi Dakta Tuni Al’ada ne ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da manema labarai a birnin Abuja, inda ya ce shugaban ƙasa Bila Tinubu yana gudanar da wasu sauye-sauye, domin samun mafita ga kalubalen da ake fuskanta tsakanin kungiyar da Gwamnatin tarayya

Dakta Alausa ya ce, gwamnati ta shiga tattaunawa kai tsaye da ASUU, inda kwamitin da Yayale Ahmed ke jagoranta ya mika shawarwari, kuma an gudanar da taron manyan jami’an gwamnati domin nazari a kai.

Ministan ya bayyana cewa an kafa kwamitin kwararru bakwai karkashin Jagorancin Sakatare Janar na Ma’aikatar Ilimi, domin daidaita matsayar gwamnati kan shawarwarin da aka gabatar.

Ya jaddada cewa gwamnatin Tinubu ba za ta rattaba hannu kan yarjejeniyar da ba za ta iya aiwatarwa ba, ko ta daure Najeriya da igiyar zato.

Ministan ya kuma ce gwamnatin Tinubu za ta ci gaba da ganin cewa ba a sake samun taƙaddama da ASUU ba, tare da tabbatar da cewa daliban Najeriya suna ci gaba da karatu ba tare da barazanar Yajin Aiki ba.

Ba dai wannan ne karon farko da kungiyar ASUUta yi yunkurin tsunduma yakin aiki a Nijeriyar ba sakamakon abin da take kira rashin cika mata alƙawarin da Gwamnatin tarayya ta zaga cikawa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
HOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna YusufYadda Hon. Hudu Kanje Ya Sake Fasalin Jagorancin Cigaban Kasa Daga Mika'il Ja'afarƳan Sanda Sun Kama Mutane 300 a Farmakin Wuraren da Ake Aikata Laifuka a FCT Sun Kwace Wukake, Bindigar Wasa, da WiwiZakari Mohammed: Dole Kwara ta Cika Kwarewarta – Dan Takarar ADC ya Nemi Muhawara a BayyaneWSCIJ ta Yaba wa PRNigeria Kan Ci Gaba da Tallafawa Matasa Wajen Sadarwa Bayan Karewar Tallafi
X whatsapp