Tawagar Amurka na Shirin Tafiya Pakistan Domin Tattaunawar Sulhu da Iran
Rahotanni daga Washington na cewa wata tawagar Amurka na shirin tashi zuwa Pakistan domin gudanar da tattaunawar sulhu da Iran.
An ruwaito Shugaban Amurka, Donald Trump na cewa yana zaton a wannan mataki babu wanda zai yi wasa da batun na shiga sulhu.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Tehran ta ce har yanzu ba ta da wani shiri kan zagaye na gaba na tattaunawar, sai dai hakan ya bar kofar bude akan yiwuwar yanke shawara a minti na karshe domin halarta.
Tsagaita wutar yakin da ake yi a yanzu tsakanin Amurka da Iran na shirin karewa a ranar Laraba.
Wakiliyar BBC ta ce shugaban Amurka Donal Trump ya ce zai yi mutuƙar wuya ya amince a ƙara wa’adin tsagaita wutar, mutsawar ba a cimma matsaya a yarjejeniyar ba.












