Home SIYASA Kalubalen da Za’a Fuskanta a Zaben 2027 – Shugaban INEC

Kalubalen da Za’a Fuskanta a Zaben 2027 – Shugaban INEC

Amupitan

Kalubalen da Za’a Fuskanta a Zaben 2027 – Shugaban INEC

FCT, Abuja – Shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, ya yi magana kan zaben shekarar 2027.

Farfesa Amupitan ya yi gargaɗin cewa yanayin rashin tsaro a sassa daban-daban na Najeriya yana barazana ga gudanar da zaɓubbuka cikin adalci da gaskiya.

Jaridar The Punch ta kawo rahoton cewa Amupitan ya yi wannan jawabin ne yayin ziyarar da ya kai wa shugaban ƴan sandan Najeriya, Tunji Disu, ranar Laraba, 6 ga watan Mayun 2026 a Abuja.

Wane kalubale ake fuskanta kan zabe?

Farfesa Amupitan ya ce ƙalubalen tsaro da ake fuskanta, waɗanda suka haɗa da tashe-tashen hankula da barazana ga tsarin zaɓe, za su iya raunana ingancin zaɓe idan ba a shawo kansu yadda ya kamata ba.

“A Najeriya, tsarin zaɓenmu ya fuskanci ƙalubale da dama tsawon shekaru, kama daga maguɗi zuwa barazanar tashin hankali, da sayen ƙuri’u waɗanda ke rage kwarin gwiwar masu zaɓe.”

“Waɗannan ƙalubalen ba wai kawai suna shafar sakamakon zaɓukanmu ba ne, har ma suna haifar da babban haɗari ga tsaron ƙasarmu.Don haka, yana da muhimmanci mu fuskanci waɗannan matsalolin da cikakken muhimmanci da azama. A kan wannan, ina so na jaddada mahimmancin ɗaukar matakan tsaro tun da wuri.”

“Yanayin rashin tsaro a sassa daban-daban na Najeriya na zama barazana ga gudanar da zaɓe cikin adalci. Yana da muhimmanci mu gudanar da cikakken binciken haɗarin tsaro gabanin zaɓen.” “Hakan zai ba mu damar gano wuraren da ake fuskantar barazana da kuma tsara dabarun da suka dace don rage haɗari, ta yadda za a kare masu zaɓe, jami’an zaɓe, da kuma mutuncin tsarin zaɓen.”

– Farfesa Joash Amupitan

Wadanne matakai INEC ke so a dauka?

A cewarsa, irin waɗannan matakan za su taimaka wajen gano wuraren da rikici zai iya tashi da kuma ba da damar tura dabarun kare masu zaɓe da jami’an zaɓe, jaridar Daily Trust ta kawo rahoton.

Farfesa Amupitan ya bayyana cewa zaɓubbukan da aka tsara gudanarwa a ranar 16 ga Janairu, 2027 (na shugaban ƙasa) da 6 ga Fabrairu, 2027 (na gwamnoni da majalisun jiha) suna buƙatar haɗin kai mai ƙarfi tsakanin INEC da hukumomin tsaro, musamman ƴan sandan Najeriya, waɗanda su ne ke jagorantar ayyukan tsaron zabe.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa'adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDPAIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da ZamfaraSojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta'addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a SokotoCOAS Shaibu ya yi Kira da a Haɗa Kai Yayin da Sojoji Ke Faɗaɗa Zuwa Rukunoni 12Najeriya ta Shirya Horarwa ta Yankuna Kan Gano da Bin Diddigin Ƙananan MakamaiSojoji Sun Kai Harin Sama da ya Hallaka Ƴan ISWAP Sama da 40, ya Lalata Motoci a BornoAmurka ta Zargi Najeriya da Daukar Yara Sojoji, Masana'antun Jarirai da Fataucin MutaneHaɗaka DMI da TMS a London ta Tsara Sabuwar Hanyar Goyon Bayan Tinubu Zuwa 2027Yushau Shuaib @57: Bikin Jagora Wanda ya Buɗe Kofofi da Canza Rayuka Daga Hafsat Ibrahim Yusha'u Shuaib @57: Barka da zagayowar Ranar Haihuwa ga Jagoran Mazaje, Mutumin da Ya Bani Dama Daga Ozumi AbdulHarin Jirgin Sama a Filin Jirgin Saudiyya ya yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 12, Raunata 309Trump ya yi Kira ga Sabon Shugaban Ukraine, ya Zargi Zelensky da Kin Amincewa da Yarjejeniyar Zaman LafiyaAFRI-CIRD ta yi Kira ga Gwamnatoci su Kara Kudin Ilimin Ƴa'ya MataAmnesty International ta yi Allah Wadai da Toshe Taron 'Dole Tinubu Ya Tafi' da Ƴan Sanda Suka yi a KanoTMG vs TMS: Matsalar Sadarwa Kan Makomar Tinubu Daga Yushau A. Shuiba 
X whatsapp