Home Labarai An Sauya Farashin Fetur a Matatar Dangote

An Sauya Farashin Fetur a Matatar Dangote

Matatar Dangote

An Sauya Farashin Fetur a Matatar Dangote

 

Jihar Legas – Matatar Man Dangote ta janye ƙarin farashin fetur da ta yi a baya, inda ta mayar da farashin kowace lita na fetur zuwa N1,275.

Sauya farashin na zuwa ne sa’o’i kaɗan bayan sanar da dillalan mai sabon farashi ga ‘yan kasuwa.

Jaridar The Punch ta ce wannan janyewar ta zo ne bayan da matatar man, a farkon ranar Laraba, 6 ga watan Mayun 2026 ta aiwatar da ƙarin farashi zuwa N1,350 kan kowace lita.

An sauya farashin fetur a matatar Dangote

Wani babban jami’i a matatar man Dangote, wanda ya buƙaci a sakaya sunansa, ya tabbatar da ƙarin farashin na farko amma ya ce matatar yanzu ta janye shi.

Ya bayyana cewa an ɗauki wannan shawarar cikin sauri ne sakamakon sauye-sauyen yanayin kasuwa, musamman faɗuwar farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya.

“An janye ƙarin farashin da aka yi a baya. Mun mayar da farashin lita zuwa N1,275,” inji jami’in.

Farashin danyen mai ya sauka Bayanai sun nuna cewa farashin ɗanyen mai ya faɗi ƙasa sosai a safiyar ranar Laraba, inda ɗanyen mai na Brent ya faɗi zuwa dala $101.7 kan kowace ganga.

An yi cinikin danyen mai na West Texas a kan dala $94.11 kan kowace ganga, wanda ke hakan ke nina raguwar kashi 7.48 cikin 100 da kashi 7.98 cikin ɗari bi da bi.

To sai dai, duk da raguwar farashin, binciken da aka gudanar ya nuna cewa gidajen mai da dama sun riga sun ƙara farashin sayarwa ga jama’a zuwa har N1,400 kan kowace lita a Legas.

Matatar Dangote ta ce ba ta yi kari ba

Jaridar The Cable ta kawo rahoton cewa matatar Dangote ta bayyana cewa farashin da take sayar da mai yana nan yadda yake.

A cikin wata sanarwa, matatar Dangote ta bayyana cewa ba ta sauya farashin ba, bayan wasu rahotanni sun nuna cewa an kara shi zuwa N1,350 kan kowace lita.

A cikin watan da ya gabata, Matatar Dangote ta sauya farashin fetur ɗinta sau da dama, sakamakon sauyin kuɗin sayo ɗanyen mai, matsin lamba na farashin canjin kuɗaɗen ƙasashen waje, da kuma yanayin rarraba man a cikin ƙasa.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
HOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna YusufYadda Hon. Hudu Kanje Ya Sake Fasalin Jagorancin Cigaban Kasa Daga Mika'il Ja'afarƳan Sanda Sun Kama Mutane 300 a Farmakin Wuraren da Ake Aikata Laifuka a FCT Sun Kwace Wukake, Bindigar Wasa, da WiwiZakari Mohammed: Dole Kwara ta Cika Kwarewarta – Dan Takarar ADC ya Nemi Muhawara a BayyaneWSCIJ ta Yaba wa PRNigeria Kan Ci Gaba da Tallafawa Matasa Wajen Sadarwa Bayan Karewar Tallafi
X whatsapp