Gwamnatin Tarayya ta Ƙaddamar da Tsarin Samun Sana’ar Kasuwanci (NEXIT CBN) na Sama da Mutane 460,000 Wanda Suka ci Gajiyar Shirin N-Power Kashi na A da B
Ministar Harkokin Jin kai Agajin gaggawa da inganta rayuwar Al’umma, Sadiya Umar Farouq, ta kaddamar da shirin zuba jari na Ƙananan Kasuwanci da Matsakaicin Kasuwancin Noma na masu fita daga shirin N-power Kashi na A da B.
Daga cikin waɗanda aka horas da su mutane 467,183 da suka nuna sha’awarsu, 75,600 za su shiga kashi na farko na shirin wayar da kan jama’a da ake sa ran za su kai ga karbar rancen kuɗi har na Naira miliyan uku daga babban bankin Najeriya idan sun cancanta.
A wajen taron kaddamar da shirin wanda aka yi a ranar Litinin ɗin da ta gabata a cibiyar ‘yan jarida da ke gidan rediyon Abuja, Ministan wanda ya samu wakilcin babban sakataren dindindin Bashir Nura Alkali ya gode wa shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa kokarin da gwamnatinsa ke yi na kawar da talauci a kasar nan da kuma tallafa wa kasar da kuma dorewar Shirye-shiryen shirin Zuba Jari a Kasar.
Ta kuma taya waɗanda za a horar mutum 467,183 wanda suka nuna sha’awar su kan shirin (NEXIT CBN AGSMEIS) daga rukunin kashi na A da B 500,000 da suka ci gajiyar shirin.
Sadiya Umar Farouq ta kula cewa wannan matakin farko ne na wasu matakai da za su gudana a dukkan jihohi 36 da kuma babban birnin tarayya Abuja.
“Burina shine kada a bar waɗanda suka kammala shirin N-power kashi na A da B ba tare da an kula da su ba. A tashoshi daban-daban, na ci gaba da tabbatar wa wadannan matasan cewa ma’aikatar kula da jin kai agajin gaggawa da inganta rayuwar al’umma ta yi aiki kafada da kafada da babban bankin Najeriya domin cimma wannan buri”.
“A yau ne aka fara wannan horon da ake jira wanda zai baiwa waɗanda suka ci gajiyar shirin samun tallafin, ga wanda suka nuna sha’awar su na shiga shirin tallafin na babban bankin Najeriya”.
Read Also:
“Don samun sauƙin aikin, za a gudanar da wannan shirin horon mataki-mataki, ina mai sanar da ku cewa dukkan Jihohi 36 da birnin tarayya sun shiga cikin wannan shiri na (NEXIT) da ake jira. Kimanin mahalarta 75,600 ne ke cikin wannan rukunin farko na horon. Za mu ci gaba da horar da ragowar rukunan nan ba da jimawa ba”.
“Ma’aikatar Jin kai, Agajin Gaggawa da inganta rayuwar al’umma ta Tarayya, ta himmatu wajen tabbatar da cewa an yi amfani da dabarun tsare-tsare na dukannin shirye-shiryen ganin cewa an bada agaji don cimma burin ta”.
“Shirin N-Power wani muhimmin bangare ne a cikin Ma’aikatar Jin kai Agajin gaggawa da inganta rayuwar al’umma, da aka tsara don cimma burin Kasa, na rage yawan talauci da samar da ayyukan yi. Shirin N-Power mabuɗi ne don taimaka wa matasan Najeriya su samu aiki da kuma haɓaka ƙwarewar rayuwa wanda ke tabbatar da cewa sun zama masu samar da mafita da ƴan kasuwa a cikin al’ummominsu”.
A jawabinsa na maraba, Babban Sakatare wanda Daraktan Tsare-tsare, Bincike da Kididdiga Raphael Oraeluno ya wakilta ya bukaci waɗanda suka ci gajiyar shirin da su yi amfani da damar ta hanyar da ta dace
“Zan so in jaddada cewa duk wanda aka horar da shi dole ne ya kalli wannan a matsayin wani dama ta musamman a matsayin wata ni’imar da ba za ayi asarar ta ba, ku tuna yadda muka yi tafiya cikin wannan shirin. A karshe kuka sami wannan damar. Ku Kula tare da bada mahimmanci a cikin duk abin da za a koya muku a cikin shirin horon. A matsayinku na masu cin gajiyar shirin, za a ba ku horon da ya dace wanda zai ba ku tabbacin shiga cikin shirin na babban bankin Najeriya”.
Ko’odinetan shirye-shiryen zuba jari na kasa Dr Umar Bindir alao ya shawarci waɗanda suka ci gajiyar shirin da su yi amfani da shirin na babban bankin Najeriya domin dogaro da kai.
A karshen horon na kwanaki biyar, waɗanda suka samu nasara za su samu bashi har na Naira miliyan uku tare da lamunin tsawon shekaru bakwai.
NNEKA IKEM ANIBEZE
SA MEDIA
14-03-2022
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 16 hours 26 minutes 35 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 18 hours 8 minutes 0 second
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com