Home Labarai Buhari na Ganawa da Tsoffin Shuwagabannin Najeriya

Buhari na Ganawa da Tsoffin Shuwagabannin Najeriya

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na jagorantar taron Majalisar Magaba a fadar Aso Rock dake birnin tarayya Abuja ranar Alhamis.

PRNigeria ta hangi Tsoffin Shugabannin Nijeriya da suka hadar da Janar Abdulsammi Abubakar (rtd) Dr. Goodluck Jonathan, da kuma Janar Yakubu Gowon (rtd), taron da aka fara karfe goma an gudanar da shine a zahiri da kuma kafar internet.

Wannan shine karo na hudu da shugaban ke jagorantar taron. An gudanar da taron farko ne a ranar 21 ga Oktoban, 2015, inda aka gudanar da karon na biyu ranar 7 ga Satumbar 2016 yayin da karo na uku ya kasance a watan August 2020.

Haka kuma sauran wadanda suka sami halartar taron sun hadar da Mataimakin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osibanjo, Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha, Mai Bawa Shugaban Kasa Shawara a sabgar tsaro Babagana Monguno, da kuma Shugaban Ma’aikatar Fadar Shugaban Kasa Farfesa Ibrahim Gambari.

Gwamnonin da suka sami halartar taron sun hadar da Gwamnan Jihar Imo Hope Uzodinma, Gwamnan Jihar Ekiti Kayode Fayemi, Gwamnan jihar Kebbi Atiku Bagudu, Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle sai kuma Gwamnan jihar Kaduna Nasir El’Rufa’i.

Kafin fara taron Majalisar Magabatan tayi shiru na minti daya don girmama ga tsohon shugaban Gwamnatin rikon kwarya, Earnest Shonekan, wanda ya rasu a 11 ga watan janairun 2022.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp