Home Labarai TSARO: Mayakan ISWAP Sun Sauya Salon kai Hare-Hare a Yankin Arewa Maso...

TSARO: Mayakan ISWAP Sun Sauya Salon kai Hare-Hare a Yankin Arewa Maso Gabas

A wani yunkuri na kawo cikas ga nasarorin da Dakarun Sojin Nijeriya ke samu akan mayakan kungiyar tada kayar baya ta Boko Haram tsagin ISWAP, mayakan sun dauki salon dasa bama bamai a kan manyan hanyoyin dake yankin Arewa Maso Gabashin Nijeriya.

PRNigeria ta gano cewa mutane da dama sun rasa rayukan su sakamakon tarwatsewar wasu nakiyoyi mafi akasarin su kirara gida da ‘yan bindigar suka binne.

Wani bincike da PRNigeria ta gudanar Ya bayyana cewa yankunan da ‘Yan da ta’addan suka binne abubuwan fashewar sun hadar da Maiduguri, Damboa, Biu, Bama, Banki, Gwoza, Buni Yadi, Malam Fatori da Kukawa.

Majiyoyin jami’an tsaro sun shaida cewa za’a dauki tsawon lokaci kafin sojoji su kammala kunce nakiyoyin dake binne a karkashin kasar.

Ko a ‘yan tsakanin nan kwamandan Operation Hadin Kai Manjo Janar Christopher Musa, ya bayyana cewa gano bazuwar bama-baman babban kalubale ne a yakin da Rundunar ke yi da masu tayar da kayar baya a yankin.

Inda yace “Dakarun Sojin sai sun bincika ko ina kafin su gudanar da ayyukan su na kakkabe ‘yan ta’addan a ko ina, sannan sai sun sake bincikawa a hanyar su ta dawowa.

By PRNigeria

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mayaƙan Lakurawa Sun Kashe Sojoji 7 a SokotoAn faɗa wa Shugaba Tinubu Cewa Ina Kitsa Yadda Zan Kashe Shi - ShettimaRundunar 'Yan Sandan Najeriya ta Ceto ƴan Mali 30 Daga Hannun Masu Safarar MutaneMun Kashe Mayaƙan ISIS 175 - Rundunar Sojin NajeriyaFarfesa Pantami ya Janye Daga Takarar Gwamnan Jihar GombeKishiya: Tsakanin ONSA na Ribadu da Tsaron Gida Famadewa Daga Yushau A. ShuaibZaben Fidda Gwani: An Harbe Mutum a Jihar PlateauRundunar 'Yan Sanda ta Tabbatar Kashe Jami'anta 17 a YobeSatar Kayayyakin Banki: An Kama Mutane Huɗu a Jihar Gombe'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Tare da Mata 2 a KatsinaJami'an Kwastam Biyu sun Rasa Ransu a Fafatawa da LakurawaMatar Aure ta Zuba wa Kishiyarta da 'Ya'yanta Biyu Fetur Tare da Banka Musu Wuta a KanoIna da ƴancin Mu'amala da Kowa ba Tare da La'akari da Jam'iyya ba - WikeAdadin Masu Fama da Cutar Tamowa na ƙaruwa a Najeriya - MSFGwamnatin Yobe ta Sha Alwashin Kawo ƙarshen Hare-Haren Boko Haram
X whatsapp