Home Labarai Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano Ta Tabbatar da Mutum 7 Sakamakon Harin...

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano Ta Tabbatar da Mutum 7 Sakamakon Harin ‘Yan Bindiga A Jihar

A kalla mutum 7 ne suka mutu sakamakon harin ‘Yan bindiga a kauyen Kurfi dake karamar hukumar Takai a jihar Kano.

Mazauna yankin sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun yi awon gaba da Dagacin Garin tare da raunata Mutum 3 a yayin harin.

Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyanawa manema labarai cewa tuni hukumar ‘Yan sandan jihar ta tura jami’an ta domin bin sahun ‘yan bindigar.

Wani shaidar gani da Ido Sale Hussaini ya bayyanawa PRNigeria cewa, ‘yan bindigar sun kaddamar da harin ranar Asabar daakrfe 11 dare, inda kai tsayi suka durfafi gidan mai Gari.

Ya bayyana sunan Dagacin Kauyen da Abdul-hayatu Ilu, inda yace guda cikin wadanda aka kashe makoci ne ga mai rike da sauatar gargajiyar.

‘Yan bindigar kuma suna halaka mutum 5 garin Tudun Makama dake makotaka da kauyen, bayan da AL’umma suka bi bayan ‘yan bindigar.

Ya kuma bayyana sunayen wadanda ‘yan bindigar suka halaka da suka hadar da Tasi’u Birniyo, Ali Yahaya, Hashimmu Amo, Sadiq hussaini, Ahmadu danlanbu, bala Audu da kuma Shu’aibu Agwar-maji.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp