Home General Gobara :Fashewar Gas Ta Yi Sanadiyyar Jakkatar Mutane 20 a Jihar Kano

Gobara :Fashewar Gas Ta Yi Sanadiyyar Jakkatar Mutane 20 a Jihar Kano

Wasu rahotannin daga jihar Kano sun tabbatar da sake samun fashewa a shagon sayar da gas ɗin girki a wata unguwa da ke cikin garin Kano, lamarin da ya jikkata mutum 20 da ƙona shaguna da dama.

Ko da yake dai wannan adadi na mutum 20 ganau ne suka tabbatarwa da PRNigeria ba hukumomin da abun ya shafa ba, duk da cewa wani bayani ya tabbatar da cewa jami’an tsaro a jihar na ganawa yanzu haka kan lamarin.

Wannan dai na zuwa ne makwanni bayan samun irin wannan fashewar a titin Aba dake unguwar Sabon Gari a Kano, inda mutum 9 da suka mutu baya ga wadanda suka jikkata.

Ko da yake a wannan lokacin an yi ta samun bayanai masu cin karo da juna, rundunar ‘yan sanda na cewa tukunyar gas ce, ganau kuma na cewa bam ne. duk da cewa daga bisani rundunar ‘yan sanda ta fito ta bayyana cewa wani mai sayar da kayan hada bam ne ya tashi da shi.

Rahotanni dai na cewa iftila’in na wannan lokaci ya faru ne a unguwar Sheka, Karshen-Kwalta.

Sai dai ganau sun ce mutum guda ya rigamu gidan gaskiya

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mayaƙan Lakurawa Sun Kashe Sojoji 7 a SokotoAn faɗa wa Shugaba Tinubu Cewa Ina Kitsa Yadda Zan Kashe Shi - ShettimaRundunar 'Yan Sandan Najeriya ta Ceto ƴan Mali 30 Daga Hannun Masu Safarar MutaneMun Kashe Mayaƙan ISIS 175 - Rundunar Sojin NajeriyaFarfesa Pantami ya Janye Daga Takarar Gwamnan Jihar GombeKishiya: Tsakanin ONSA na Ribadu da Tsaron Gida Famadewa Daga Yushau A. ShuaibZaben Fidda Gwani: An Harbe Mutum a Jihar PlateauRundunar 'Yan Sanda ta Tabbatar Kashe Jami'anta 17 a YobeSatar Kayayyakin Banki: An Kama Mutane Huɗu a Jihar Gombe'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Tare da Mata 2 a KatsinaJami'an Kwastam Biyu sun Rasa Ransu a Fafatawa da LakurawaMatar Aure ta Zuba wa Kishiyarta da 'Ya'yanta Biyu Fetur Tare da Banka Musu Wuta a KanoIna da ƴancin Mu'amala da Kowa ba Tare da La'akari da Jam'iyya ba - WikeAdadin Masu Fama da Cutar Tamowa na ƙaruwa a Najeriya - MSFGwamnatin Yobe ta Sha Alwashin Kawo ƙarshen Hare-Haren Boko Haram
X whatsapp