Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai hari a rukunin gidaje dake bayan EFAB dake Gwarinfa, wani yanki dake kwaryar birnin.
Maharan dauke da muggana makamai da suka hadar da kibbau, adduna da sauransu sun dira cikin rukunin gidajen ne da sanyin safiyar litinin.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Wannan harin na zuwa ne sa’oi kadan bayan da wasu mahara suka kai hari kan wata majami’a a kauyen Owo dake jihar Ondo a kudancin Najeriyar.
ko da muka tuntubi jami’ar hulda da jama’a ta rundunar ‘yan sandan birnin na Abuja Josephine Adeh tace basu tabbatar da harin na garkuwa da mutane ne ko kuma na fashi da makami, ta kuma bayyana cewa da zarar sun kamala bincike za tayi bayani.












