Home General Zaman Gida: Mayakan IPOB Sun Kone Motar Siminti a Jihar Enugu

Zaman Gida: Mayakan IPOB Sun Kone Motar Siminti a Jihar Enugu

‘Yan bindiga da ake zargin mambobin haramtacciyar kungiyar ‘yan awaren biyafara ce dake gudanar da ayyukan ta a Kudu Maso Gabashin Nijeriya, a wani bangare na tabbatar da kudirin zaman gida dole ga Al’ummar yankin sun kone Motar siminti ta Dangote makare da kaya a mahadar Beach dake karamar hukumar Nsukka dake Jihar Enugu kasar.

Wasu mazauna yankin da suka bukaci a sakaye sunansu, sun bayyana cewa lamarin ya auku ne da misalin karfe 5:30 na Asubahi inda Al’ummar yankin ke tsaka da bacci.

Duk da dai ba’a rasa rai ba amma dai an rawaito cewa maharan sun lakadawa matukin motar dukan kawo wuka, inda daga bisani suka kuma sakeshi ya tafi.

“Na ji kukan wani wanda daga bisani na fahimci direban motar ne. Abu na gaba da na gani kuma shine hayaki na tashi daga motar, wanda ke alamta a kunna mata wuta, kamar yadda majiyar ta tabbatar, a cewar wani mazaunin yankin.

PRNigeria ta rawaito cewa bayan sun bar wajen ne wasu daga cikin Al’umma suka kashe wutar domin hana cinye motar, kasancewar motar na dauke da simintin na miliyoyin Naira.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp