Home Labarai ‘Yan Ta’adda Sun Afka Asibitin UNIOSUN Domin Kwato Gawar Dan Uwansu

‘Yan Ta’adda Sun Afka Asibitin UNIOSUN Domin Kwato Gawar Dan Uwansu

Wasu da ake zargin ‘Yan Ta’adda ne sun yiwa Asibitin Koyar na Jami’ar Jihar Osun dake garin Osogbo tsinke, domin daukar gawar guda cikin abokan ayyukan ta’addanci su da ya mutu sakamako Harbin bindiga.

An ruwaito cewa mutum 2 ne suka mutu sakamakon harin na ‘yan bindigar a ranar talata a garin na Osogbo, sai dai jami’an tsaro na Amotekun sun sami nasarar kama guda cikin ‘yan Daban.

Daga bisani wasu daga cikin ‘yan ta’addan sun lalata gidan kwamandan Amotekun, Amitolu Shittu, a yayin artabun ne guda cikin su ya sami raunukan Harbin bindiga kuma an kai shi asibitin koyarwa na UNIOSUN domin yi masa magani daga bisani yace mutu.

Majiyar mu ta rawaito cewa ‘yan bindigar sun mamaye asibitin ne da nufin dauko gawar abokin aikinsu amma jami’an kiwon lafiya suka dage kan a basu cikakkun takardu, wanda ‘yan ta’addan suka yi biris da bukatar jami’an asibitin.

Wani shaidar gani da Ido yace, ‘yan ta’addan sun kara karfi inda suka kutsawa cikin harabar Asibitin da muggana makamai da suka hadar da Gatari, Katako, Wukake da dai sauran makamai masu razanarwa, wannan ta sanya jami’an asibitin rufe manyan kofofin asibitin na tsawon sa’oi 2 abinda ya hana su dauke gawar.

Likitoci da ma’aikatan jinya da sauran ma’aiktan asibitin sun nemi mafaka kafin jami’an tsaro su shiga Tsakani.

Shugaban kwamitin ba da shawara a Asibitin koyarwa na Jami’ar Jihar Osun, Osogbo, Babatunde Afolabi ya tabbatar da faruwar lamarin amma y ace ‘an shawo kan matsalar; bayan sun gudanar da bincike kan gawar an fitar da ita domin binne wa.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp