Home Labarai ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Sojoji Da Fararen Hula A Jihar Niger

‘Yan Bindiga Sun Hallaka Sojoji Da Fararen Hula A Jihar Niger

Akalla fararen hula mutum 43 ne suka mutu wanda suka hadar da sojojin 30 da ‘yan sandan kwantar da tarzo 7 sakamakon harin ‘yan bindiga a wani wurin hakar ma’adanai  a karamar hukumar Shiroro dake jihar Nijer, kamar yadda wata majiya ta shaida mana.

A yayin da gwamnatin jihar ta Niger ke tabbatar da faruwar harin, ta bayyana cewa bata kai ga gano adadin wadanda harin ya rutsa dasu ba.

Mazauna yakin sun bayyana cewa jami’an Bincike sun gano gawarwakin sojoji da Jami’an ‘yan sandan 37 yashe a cikin daji ranar Alhamis, gami da gawarwakn fararen hula 6 duk a cikin dajin.

Mazauna yankin sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun yi awon gaba da ‘yan Nijeriya da ‘yan kasar Sin (Chaina) da dama a yayin harin da suka kai wajen hakar ma’adanan a ranar laraba.

Yusuf Kokki, wanda gudana ne cikin shuwagabannin kungiyar Matasan Shiroro, ta cikin wata sanarwa da ya aikewa manema labarai yace mazauna wurin sun shaida harin maharan dauke da muggan makamai.

Ya tabbatar da cewa lamarin ya faru ne yayin da ‘yan bindigar suka yiwa wurin hakar ma’adanan tsinke, nan suka fara harbi kan mai uwa da wabi akan ma’aikatan da masu tsaron lafiyar su.

Ya ce mazauna yankin zasu zakulo Karin wasu gawarwakin a aikin da suke cigaba da yi na nemo wadanda harin ya rutsa dasu.

Yace jami’an ‘yan sandan kwantar da tarzoma 7 sun mutu da wasu Karin fararen hula guda 6 a wajen hakar ma’adanan.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mayaƙan Lakurawa Sun Kashe Sojoji 7 a SokotoAn faɗa wa Shugaba Tinubu Cewa Ina Kitsa Yadda Zan Kashe Shi - ShettimaRundunar 'Yan Sandan Najeriya ta Ceto ƴan Mali 30 Daga Hannun Masu Safarar MutaneMun Kashe Mayaƙan ISIS 175 - Rundunar Sojin NajeriyaFarfesa Pantami ya Janye Daga Takarar Gwamnan Jihar GombeKishiya: Tsakanin ONSA na Ribadu da Tsaron Gida Famadewa Daga Yushau A. ShuaibZaben Fidda Gwani: An Harbe Mutum a Jihar PlateauRundunar 'Yan Sanda ta Tabbatar Kashe Jami'anta 17 a YobeSatar Kayayyakin Banki: An Kama Mutane Huɗu a Jihar Gombe'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Tare da Mata 2 a KatsinaJami'an Kwastam Biyu sun Rasa Ransu a Fafatawa da LakurawaMatar Aure ta Zuba wa Kishiyarta da 'Ya'yanta Biyu Fetur Tare da Banka Musu Wuta a KanoIna da ƴancin Mu'amala da Kowa ba Tare da La'akari da Jam'iyya ba - WikeAdadin Masu Fama da Cutar Tamowa na ƙaruwa a Najeriya - MSFGwamnatin Yobe ta Sha Alwashin Kawo ƙarshen Hare-Haren Boko Haram
X whatsapp