Kamfanin Emirates ya soke zirga-zirga zuwa Nijeriya

Kamfanin sufurin jiragen sama na Emirates ya soke zirga-zirga zuwa Najeriya saboda kuɗaɗensa da ya ce gwamnatin ƙasar ta hana shi taɓawa.

Kamfanin na Daular Larabawa ya ƙara da cewa har yanzu bai samu kasonsa ba na dala miliyan 260 da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sakar wa kamfanonin ƙasar waje na kuɗin tikiti da suka sayar a Najeriyar.

A watan Satumba ne Emirates ya koma zirga-zirga a Najeriya bayan CBN ya sanar da sakin kuɗin, wanda wani ɓangare ne na fiye da dala miliyan 600 da kamfanonin jiragen ke son kwashewa zuwa ƙasashensu na asali.

“Har yanzu Emirates bai samu nasa kason ba daga cikin kuɗin da ya kamata ya kai gida,” a cewar sanarwar da ya fitar ranar Alhamis.

“Idan ba a kwashe kuɗin zuwa gida ba kuma ba tare da wani tsarin da zai tabbatar da cewa kuɗaɗen ba su ci gaba da taruwa ba…ba za mu iya ci gaba da aiki ba balle ma zirga-zirgarmu zuwa Najeriya.”

Ko da yake dai ana kallon wannan mataki na kamfanin matsayin wani bangare na rashin jituwar dake tsakanin daular larabawan da Nijeriyar duk da kamfanin bai fito karara ya bayyana hakan ba.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1254 days 22 hours 1 minute 55 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1236 days 23 hours 43 minutes 20 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com