Rundunar sojin saman Najeriya ta kai wani samame ta sama a kan wasu gungun ƴan bindiga da aka gano a wasu wuraren da ke cikin wasu kananan hukumomin Kaduna, inda suka hallaka da dama da ga cikin su.
wannan na kunshe ta cikin wata sanarwa da Kwamishinan tsaro da harkokin cikin , Samuel Aruwan, ya fitar aka raba ga manema labarai.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Ya ce an yi luguden wutar a kan ƴan ta’addan ne a yankin Kawara da ke karamar hukumar Igabi a wuraren da ‘yan bindigar samu maɓoya.
“An tabbatar da kashe ‘yan bindiga a harin na jirgin sama kuma wasu da aka yi garkuwa da su sun samu tserewa daga yankin gaba daya, kamar yadda wasu majiyoyi masu sahihanci na suka tabbatar.
“Hakazalika, a Walawa, karamar hukumar Giwa, an kai hari a wani wuri da aka yi nasarar gano wa. A karamar hukumar Chikun, an gudanar da aikin sa ido a kan Faka, Kangon Kadi, Damba, Ungwan Turai, Galbi, Gwagwada da kewaye. An ga ‘yan ta’adda a nisan kilomita 4 daga Arewa maso Yamma da Godani, kuma duk an kashe su,” inji shi. Aruwan ya ci gaba da cewa a Kuduru, an ga inda ‘yan ta’addan suka kai hari da rokoki.
Ya ce a karamar hukumar Igabi, an gudanar da ayyuka a kan Riyawa, Alhaji Isiaka, Rima, Riyawa, Rumana, Ungwan Liman, Mai Gishiri da kuma yankin filin jirgin sama na Kaduna ba tare da sojojin sun raunata ba.
Ya kuma kara da cewa an samu irin wannan lamarin a Sabon Birnin, Anaba, Malumi, Wusono da Kerawa.
PRNigeria Hausa












