Burtaniya ta Gargadi ‘Yan Siyasar Nijeriya

Gwamnatin Birtaniya ta sake gargadin ‘yan siyasar Najeriya da ke tunzira magoya bayansu wajen tada hankali ko kuma rikicin da ke kai ga rasa rayuka da su kwan da sanin cewar ba za ta ba su izinin shiga kasarta ba.

Wannan na zuwa ne gabatowar babban zaben kasar, wanda wasu cikin ‘yan siyasar ke amfani da damar wajen tada tarzoma lura da yadda irin wadannan matsaloli ke yi wa shirin zaben shekarar 2023 barazana.

Babbar Jami’ar Diflomaisyar kasar Catriona Lang ta bayyana haka lokacin da ta jagoranci tawagar manyan jami’anta domin ganawa da shugabannin ‘yan kwamitin zartarwar jam’iyyar adawa ta PDP.

Lang ta ce zaben shekarar 2023 na da matukar muhimmanci ga Afirka da kuma duniya baki daya, saboda haka hankalin Birtaniya da kuma kasashen duniya ya karkata akan kasar.

Jami’ar ta ce Birtaniya ta yi matukar damuwa da irin laifuffukan da ke da nasaba da zabe 52 da aka gani a jihohi daban-daban har 22, ciki har da harin da aka kai wa tawagar jam’iyyar PDP a Jihar Borno.

Lang ta ce suna cike da damuwa akan irin wadannan tashe-tashen hankula, saboda haka suka bukaci tattaunawa da shugabannin jam’iyyar akan irin matakan da suka dace a dauka domin tabbatar da ganin an yi zaben cikin kwanciyar hankali.

Birtaniya ta ce yana da wahala mutane su fito su yi zabe muddin suna fuskantar takala ko barazana, yayin da wadannan abubuwa na iya shafar kimar zaben baki daya.

Lang ta ce za su ci gaba da sanya ido akan ‘yan siyasar da ke tada hankali ko kuma tinzira jama’a tada hankalin wajen amfani da kafofin yada labarai daga kowacce jama’iyya domin daukar mataki akansu.

PRNigeria Hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1239 days 16 hours 50 minutes 26 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1221 days 18 hours 31 minutes 51 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com