Dakarun Rundunar sojin saman Nijeriya sun sami nasarar tarwatsa maboyar ‘yar Ta’adda a kananan hukumomin Chikum da Igabi a jihar kaduna.
Wannan na kunshe ta cikin wata sanarwa da kwamishinan tsaro da al’amarun cikin gida na jihar Samuel Aruwan ya fitar.
Sanarwar tace a wani bangare na atisayen kawar da ‘yan ta’adda a fadin jihar, Dakarun sojin Nijeriya sun tabbatar da tarwatsa maboyar ‘yan ta’addan tare da tarwatsa ‘yan Ta’addan a wani sabon hari.
Haka kuma dakarun sun tarwatsa wata maboyar da makamin roket a maboyar su dake dajikan Kofita da Kuyanbana na karamar hukumar Birnin Gwari.
Da kuma wasu maboyar su a Kuduru da Gonan Baturiya dske nisan kilomita 4 yamma da Nabango.
A yayin da dakarun ke gudanar da atisaye a yankunan Karshi, Kerawa da Walawa a kananan Hukumomin of Igabi da Giwa inda aka hangi maboyar taso mai nisan kilomita 6 gudu maso yammacin Kerawa.
Gwamnatin jihar Kaduna ta karbu rahoton tare da yabawa dakarun sojin bisa namijin kokarin su na kawar da ‘yan ta’adda a jihar
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1190 days 11 hours 40 minutes 17 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1172 days 13 hours 21 minutes 42 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com