Home General Za’a Nada Ambasada Ahmad Rufa’i Matsayin Sabon ‘Sardaunan Katsina’

Za’a Nada Ambasada Ahmad Rufa’i Matsayin Sabon ‘Sardaunan Katsina’

Majalisar Masarautar Katsina ta sanarwar da tsare-tsare nadin sabon sardaunan Katsina, Ambassador Ahmed Rufa’i Abubakar.
Guda cikin Mambobin Majalisar ne ya bayyanawa PRNigeria cewa sabon sardaunan wanda shine babban Daraktan hukumar tsaro da bayanan sirri ta Nijeriya (NIA) wanda za’ayi bikin ranar 31 ga watan Disambar 2022 a fadar Mai Martaba sarkin katsina dake Jihar.
Majalisar ta fayyace cewa sarautar ta sardauna ana alakanta ta ne da Tsohon Firaministan jihar Arewa Sir Ahmadu Bello, wanda ba mutum ne zai bukaci cewa a nadashi ba, Majalisar tace ana duba jajircewa, da farin jini da kuma cancantar mutum, gami da hangen nesa na mai martaba sarkin Katsina Alhaji (Dr) Abdulmumini Kabir Usman, CFR, wanda ya aro Sardaunan daga Masarautar sokkwato domin kara kare ta a tarihi.
Shirye-shiryen nadin dai zai fara ne da wasan dawaki a ranar 27 ga watan December, 2022 a Rubicon Polo and Resorts Centre, Idu, Abuja, sai kuma wasan Golf da zai biyo baya a filin wasan Golf na Katsina a 28 ga watan December.
Daga ranar 29 zuwa 30 ga watan Disambar kuwa za’a gudanar taro mai taken Al’adu da martabarsu, da batutuwa kan tarihin Katsina, a babban daki taro na Katsina Motel.
Yayin da mai martaba sarkin Katsina Alhaji Abdulmuminu Kabir Usman CFR, zai jagoranci nadin a fadarsa da karfe 10 na safe.
PRNigeria Hausa

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Manyan Tsofaffin Jami'an Soji 10 da Suka Rasa Rayukansu a Hannun ƴan Ta'addaTarihin Rayuwar Janar Rabe da ya Rasu a Hannun ƴan BindigaMatsalar Tsaro: Masu Zanga-Zanga Sun Tare Babbar Hanyar AbujaDuk Wanda aka Kama Yana Kasuwanci da 'Yan Ta'adda, za a ɗauke shi a Matsayin ɗan ta’adda - Christopher MusaFarashin ɗanyen Mai ya Faɗi Bayan Amurka ta Soke Sabbin Hare-Haren kaiwa IranAmurka ta yi sulhu kan yaƙin da ta ke yi da Iran - TrumpMajalisar Wakilan Najeriya ta Amince da ƙudirin Dokar Kafa ’Yan sandan JihaHukuncin da aka Yanke wa Masu Alaƙa da Sace ɗaliban Jihar NejaMiyagun ƙwayoyi da Makamai: Jami'an Tsaro Sun Kama Mutane 8 a Jihar YobeAbin da Obi ya Fada Kan Atiku - Dele MomoduHukumar EFCC ta Gurfanar da Ma'aurata Kan Damfarar Kudi Kusan N2bnFiye da Kashi 60 na 'Yan Najeriya a Yanzu Suna Rayuwa Cikiin Fatara - IMFGwamnatin Najeriya ta Caccaki Afrika ta Kudu kan Harin da ake yi wa ƴan ƙasartaƳan Bindiga sun Buƙaci Kudin Fansa Kafin Sako Dattijan da Suka je Sulhu a ZamfaraMayaƙan Lakurawa Sun Kashe Sojoji 7 a Sokoto
X whatsapp