Home General Sojojin Najeriya sun hallaka mayakan kungiyar boko haram 140 a cikin watan...

Sojojin Najeriya sun hallaka mayakan kungiyar boko haram 140 a cikin watan Disamban 2022

Sojojin Najeriya sun hallaka jimullar mayakan kungiyar boko haram kimanin 140 a cikin watan Disamban 2022.
An kashe adadin mutanen ne a hare-haren da aka kai tsakanin ranar daya zuwa 22 ga watan, sannan kuma an ji wa wasu da dama munanan raunuka.
A cewar Zagazola Makama, kwararre kuma mai sharhi kan al’amuran tsaro a yankin Tafkin Chadi, rundunar sojan kasa da na sama na Operation HADIN KAI sun ci gaba da mamaye yankin gaba daya na ayyukansu.
Ya ce an sami nasarar ce a kauyuka da garuruwa da tsaunuka da ke cikin Kananan Hukumomin Damboa, Bama, Gwoza da Konduga na jihar Borno, da kuma na Gulani da Geidam dake Jihar Yobe.
A cewar Zagazola, musamman a ranar 1 ga Disamba, 2022, sojoji sun gwabza da ’yan ta’addan Boko Haram dana tsagin ISWAP a Damboa ta jihar Borno.
Dakarun da ke samun goyon bayan jiragen sama sun yi artabu da ’yan ta’addan tare da kashe da dama yayin da sauran suka gudu da manyan raunuka a jikinsu.
Sojojin sun yi amfani da dabaru yaki inda suka kwato bindigogi kirar AK47 guda shida, bindigogin FN 3, bindigogin kirar QJC guda 2, alburusai 102 masu tsayin 12.7mm, 2,152 na musamman na 7.62mm na musamman, 20 masu tsayin 7.62mm NATO, bututu 1 RPG, bam 1 HEAP, 1 HEAP Bom.
Sauran makaman da aka kwato sun hada da bam da gurneti na hannu.
Sojojin sun kuma samu nasarar kwato daya daga cikin motar ’yan ta’addan tare da lalata wata motar bindiga guda daya.
Hakazalika, a ranar biyu ga Disamba, 2022, sojojin da ke sintiri na yaki sun yi karo da ‘yan ta’adda a yayin da suke yin amfani da dajin da ke wajen garin Mallam Fatori a Karamar Hukumar Abadam ta jihar Borno.
A yayin musayar wuta a wannan hari sojoji sun kashe ’yan ta’adda biyar tare da kama daya.
Har ila yau, a ranar 11 ga Disamba, 2022, sojoji sun kama kwamandojin ’yan ta’addar Boko Haram hudu a kan hanyar Gwoza zuwa Yamteke a Karamar Hukumar Gwoza ta jihar Borno.
An bayyana cewa sun tsere ne daga Sabil Huda da ke dajin Sambisa saboda tsananin ruwan bama-bamai da dakarun nasu suka yi.
Abubuwan da aka kwato daga hannun ’yan ta’adda sun hada da bindigogin AK-47 guda uku, bindiga korar G3 guda daya, da alburushi 20 na musamman na 7.62mm, harsashi guda 12 da wayoyin hannu guda biyu da tsabar kudi Naira 125,400 da sauran kayayyaki.Sojojin Najeriya sun hallaka jimullar mayakan kungiyar boko haram kimanin 140 a cikin watan Disamban 2022.
An kashe adadin mutanen ne a hare-haren da aka kai tsakanin ranar daya zuwa 22 ga watan, sannan kuma an ji wa wasu da dama munanan raunuka.
A cewar Zagazola Makama, kwararre kuma mai sharhi kan al’amuran tsaro a yankin Tafkin Chadi, rundunar sojan kasa da na sama na Operation HADIN KAI sun ci gaba da mamaye yankin gaba daya na ayyukansu.
Ya ce an sami nasarar ce a kauyuka da garuruwa da tsaunuka da ke cikin Kananan Hukumomin Damboa, Bama, Gwoza da Konduga na jihar Borno, da kuma na Gulani da Geidam dake Jihar Yobe.
A cewar Zagazola, musamman a ranar 1 ga Disamba, 2022, sojoji sun gwabza da ’yan ta’addan Boko Haram dana tsagin ISWAP a Damboa ta jihar Borno.
Dakarun da ke samun goyon bayan jiragen sama sun yi artabu da ’yan ta’addan tare da kashe da dama yayin da sauran suka gudu da manyan raunuka a jikinsu.
Sojojin sun yi amfani da dabaru yaki inda suka kwato bindigogi kirar AK47 guda shida, bindigogin FN 3, bindigogin kirar QJC guda 2, alburusai 102 masu tsayin 12.7mm, 2,152 na musamman na 7.62mm na musamman, 20 masu tsayin 7.62mm NATO, bututu 1 RPG, bam 1 HEAP, 1 HEAP Bom.
Sauran makaman da aka kwato sun hada da bam da gurneti na hannu.
Sojojin sun kuma samu nasarar kwato daya daga cikin motar ’yan ta’addan tare da lalata wata motar bindiga guda daya.
Hakazalika, a ranar biyu ga Disamba, 2022, sojojin da ke sintiri na yaki sun yi karo da ‘yan ta’adda a yayin da suke yin amfani da dajin da ke wajen garin Mallam Fatori a Karamar Hukumar Abadam ta jihar Borno.
A yayin musayar wuta a wannan hari sojoji sun kashe ’yan ta’adda biyar tare da kama daya.
Har ila yau, a ranar 11 ga Disamba, 2022, sojoji sun kama kwamandojin ’yan ta’addar Boko Haram hudu a kan hanyar Gwoza zuwa Yamteke a Karamar Hukumar Gwoza ta jihar Borno.
An bayyana cewa sun tsere ne daga Sabil Huda da ke dajin Sambisa saboda tsananin ruwan bama-bamai da dakarun nasu suka yi.
Abubuwan da aka kwato daga hannun ’yan ta’adda sun hada da bindigogin AK-47 guda uku, bindiga korar G3 guda daya, da alburushi 20 na musamman na 7.62mm, harsashi guda 12 da wayoyin hannu guda biyu da tsabar kudi Naira 125,400 da sauran kayayyaki.

PRNigeria hausa

VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp