Jami’an agaji a yankin Darfur na ƙasar Sudan sun ce akalla mutane takwas ne suka mutu a rikicin da ya ɓarke a cikin dare tsakanin wasu al’ummomin da ke zaman doya da manja.
Da farko dai an fara harbe-harbe ne a garin Zalingei, daga bisani ‘yan kabilar Rizeigat ta Larabawa, da suka kai hari wani sansanin ‘yan gudun hijira na ‘yan kabilar Fur, a kan babura.
Read Also:
Ɓarkewar tashe-tashen hankula sun karu tun bayan janyewar tawagar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a bara.
Har yanzu dai yankin na Darfur bai farfaɗo ba daga yaƙin da ya sha fama da shi tun kusan shekaru ashirin da suka gabata, wanda ya raba sama da mutane miliyan biyu da gidajensu.
Ana zargin da sa hannun wasu mayakan sa kai da ke samun goyon bayan gwamnati a wasu hare-haren da ake kaiwa.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1255 days 1 hour 30 minutes 38 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1237 days 3 hours 12 minutes 3 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com