Babban Sifeton ‘yan sandan Najeriya Usman Alkali Baba, ya gana da gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu a shelkwatar hukumar ‘yan sandan ƙasar da ke Abuja babban birnin ƙasar, domin tattauna wasu batutuwa ciki har da batun yin adalci ga lauyar nan da wani jami’an ɗan sanda ya harbe a birnin Legas ranar Kirsimeti.
Read Also:
A cikin wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan ta fitar mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na rundunar ya ce babban sifeton ‘yan sandan, ya jadda cewa za a gudanar da cikakken bincike tare da alƙawarin yin adalci game da batun, yana mai cewa hukumar na aiki kafaɗa-da-kafaɗa da ofishin babban lauyan gwamnatin jihar Legas domin tabbatar da an gurfanar da wanda ke da hannu a gaban kotu.
A nasa ɓangare gwamnan jihar Legas ɗin ya alkawarta taimaka wa rundunar ‘yan sandan domin ganin cewa an yi adalci game da binciken kisan lauyar.
Tuni dai babban Sifeton ‘yan Sandan ƙasar ya bayar da umarnin dakatar da jami’in ɗan sandan da ya harbe tare da kashe lauyar mai suna Omobolanle Raheem a birnin Legas.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1255 days 1 hour 38 minutes 14 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1237 days 3 hours 19 minutes 39 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com