Home General Buhari: Kamfanin samar da karafa na Ajaokuta zai ke samar da $1.6bn...

Buhari: Kamfanin samar da karafa na Ajaokuta zai ke samar da $1.6bn tare da sabbin masu zuba jari duk shekara.

Shugaban Nijeriya Muhammad Buhari yace kamfanin samar da karafa na Ajakuta zai ke samar da dala biliyan 1.6 dukkan shekara tare da samar da guraban ayyuka ga matasan kasar.
Wannan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da Mai Magana da yawun shugaban kasar Malam garba shehu ya fitar, wadda tace shugaban kasar ya bayyana hakan ne a fadar ohinoyi na garin Ebira, wanda kuma ya kaddamar da ziyarar aiki ta kwana guda a garin Okene na jihar kogi ranar Alhamis.
Shehu ya bayyana cewa Buhari ya magantu kan kudirin gwamnatin sa na mayar da jihar kogi matsayin cibiyar masana’antu kuma jihar da zata zama wajen samar da albakatun kasa.
Shugaban ya bayyana yadda gwamantin tarayya ta cimma matsaya kan dukkan wata doka da zata kawo tasgaro ga ciban kamfanin samar da karafan na Ajaokuta.
Inda yace aikin zai matukar amfanar da Al’ummar jihar
Shugaban y ace jihar kogi za kuma ta ci gajiyar aikin ta hanyoyi daban-daban musamman idan bututun iskar gas na AKK daya ratsa ta cikin jihar mai tsawon kilmita 614 (mil 384) wanda ake sa ran fara aikin sa a shekarar 2023.
Ya kuma bayyana cewa jam’iyyar sa ta APC ta cika dukkan Alkawuran data daukarwa Al’ummar Nijeriya a ko wanne mataki.
Daga bisa ya bayyana cewa gwamnan jihar Yahaya Bello yayi abin a yaba a lokacin mulkinsa na tsahon shekaru 8 wato zango biyu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp