Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta sami Nasarar kama ‘yan daban Siyasa 61 dauke da makamai a jihar.

Rundunar ‘yan sandan jihar kano ta sami Nasarar kama ‘yan daban Siyasa 61 dauke da makamai a jihar.

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta sami nasarar kama ‘yan daba 61 dauke da makamai da ake zargi da tada hargitsi, a kokarin rundunar dajike dukkan ayyukan Ta’addanci lokaxin yakin neman zabe.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Mamman Dauda, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da kakakin rundunar SP Abdullahi Haruna-Kiyawa, ya raba manema labarai a Kano.

Yace kame ya biyo baya umarnin babban sifeton
Janar na ‘yan sanda Nijeriya Usman Alkali-Baba, domin tabbatar da gudanar da ingantaccen zabe gami da dakile ayyukan daba a yayin zabe.
“wadanda ake zargin an kamasu ne a ranar 4 ga watan Janairu, yayin wani atasaye kakkabe barna a lokacin yakin neman zabe a filin wasa na Sani Abacha.

Yace an kwato makamai a hannun wadanda ake zargin da suka hadar da wukake 33, adduna 8, almakashi 4 sai kuma kunshin tabar wiwi guda 117.
Kwamishinan ya kara da cewa, kafin a fara gudanar da aikin, an gudanar da taron kwamitin tuntuba tsakanin hukumomin tsaro kan harkokin zabe da kuma taron zaman lafiya da ya kunshi dukkan masu ruwa da tsaki.
“An kuma gudanar da tarurruka da masu ruwa da tsaki akan zabe a kananan hukumomi, da kuma ofishoshin ‘yan Sanda.
“Shugabannin jam’iyyar siyasa da ‘yan takarkaru sun yi alkawarin bawa ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro hadin kai a jihar domin samun ingantaccen zabe mai inganci,” in ji shi.
Dauda ya yabawa al’ummar jihar da sauran hukumomin tsaro da kafafen yada labarai da kungiyoyin ‘yan masu zaman kansu da masu ruwa da tsaki a harkar ‘yan sanda bisa addu’o’i da goyon baya da karfafa gwiwa da hadin kai.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1254 days 21 hours 50 minutes 45 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1236 days 23 hours 32 minutes 10 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com