Home General Yara sama da miliyan 30 na fuskantar Barazanar Yunwa a sassan Duniya

Yara sama da miliyan 30 na fuskantar Barazanar Yunwa a sassan Duniya

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci daukar matakan gaggawa don ceto yara fiye da miliyan 30 da ke fuskantar barazanar cutar yunwa a kasashe 15 da ke fama da matsananciyar yunwa ciki har da Najeria Sanarwar wadda sassan lafiya da abinci da kuma kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya 5 suka fitar sun yi gargadin cewa matukar ba a dauki matakan da suka kamata ba, ko shakka babu yaran fiye da miliyan 30 za su fuskanci cutar yunwa sakamakon rashin abinci mai gina jiki.

Sanarwar ta Majalisar Dinkin Duniya da ke wannan gargadi ta zayyano kasashen da za su fuskanci wannan matsala ciki har da Afghanistan da Burkina Faso da Chadi da Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo baya ga Habasha da Haiti da Kenya da kuma Madagascar sai kasashen Mali, Nijar, Najeriya da Somalia da Sudan ta kudu kana Sudan da Yemen.

Sassan na Majalisar 5 da suka kunshi hukumar abinci ta duniya FAO da mai kula da bakin haure UNHCR da kuma asusun tallafawa kananan yara na UNICEF da WHO baya ga shirin samar da abinci na duniya WFP sun ce wajibi ne a hada hannu don hana faruwar wannan annoba da ke tunkaro Duniya.

A cewar sanarwar sassan 5 cutar ta yunwa ko kuma rashin abincin mai gina jiki ga kananan yara na sahun cutukan da ke haddasa asarar rayukan miliyoyin yara kowacce shekara musamman a matalautan kasashe ko kuma wadanda yaki ko matsalar tsaro ta daidaita.

Sassan Majalisar sun bayyana cewa wajibi ne Duniya ta mike tsaye don tunkarar matsalar da nufin ceto yaran fiye da miliyan 30 wadanda rayuwarsu ke halin tsaka mai wuya saboda karanci ko kuma rashin abincin mai gina jiki baki daya.

PRNigeria hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa'adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDPAIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da ZamfaraSojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta'addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a SokotoCOAS Shaibu ya yi Kira da a Haɗa Kai Yayin da Sojoji Ke Faɗaɗa Zuwa Rukunoni 12Najeriya ta Shirya Horarwa ta Yankuna Kan Gano da Bin Diddigin Ƙananan MakamaiSojoji Sun Kai Harin Sama da ya Hallaka Ƴan ISWAP Sama da 40, ya Lalata Motoci a BornoAmurka ta Zargi Najeriya da Daukar Yara Sojoji, Masana'antun Jarirai da Fataucin MutaneHaɗaka DMI da TMS a London ta Tsara Sabuwar Hanyar Goyon Bayan Tinubu Zuwa 2027Yushau Shuaib @57: Bikin Jagora Wanda ya Buɗe Kofofi da Canza Rayuka Daga Hafsat Ibrahim Yusha'u Shuaib @57: Barka da zagayowar Ranar Haihuwa ga Jagoran Mazaje, Mutumin da Ya Bani Dama Daga Ozumi AbdulHarin Jirgin Sama a Filin Jirgin Saudiyya ya yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 12, Raunata 309Trump ya yi Kira ga Sabon Shugaban Ukraine, ya Zargi Zelensky da Kin Amincewa da Yarjejeniyar Zaman LafiyaAFRI-CIRD ta yi Kira ga Gwamnatoci su Kara Kudin Ilimin Ƴa'ya MataAmnesty International ta yi Allah Wadai da Toshe Taron 'Dole Tinubu Ya Tafi' da Ƴan Sanda Suka yi a KanoTMG vs TMS: Matsalar Sadarwa Kan Makomar Tinubu Daga Yushau A. Shuiba 
X whatsapp