Home General Zargin sayar da Man Fetur Ba bisa ka’ida ba ya haddasa Gobara...

Zargin sayar da Man Fetur Ba bisa ka’ida ba ya haddasa Gobara a Gidan Man NNPCL Na Jihar Kano

Zargin sayar da man fetur ba bisa ka’ida bay a haddasa tashin wata gobara a gidan mai mallakin kamfanin NNPCL dake shatale-talen kano Club dake jihar kano a Arewa maso yammacin Nijeriya.
Wannan dai iftila’I na zuwa ne daidai lokacin da Al’umma jihar da wasu jihohihin dake kasar ke fama da matsalar karanci da tsadar manfetur sakamakon rashin tartibin farashin sa.
Shaidun gani da ido sun tabbatar wa da PRNigeria cewa bayan kammala zuba man ne a wata mota kirar Sienna wadda aka yi mata Karin tanki ne lamarin ya auku.
Sai dai duk da kokarin hukumar kashe gobara na dakile yaduwar gobarar lamarin sai da ya kai ga konewar motar kurmus.
Wani shaida ma da lamarin ya faru gaban idon sa wanda ya bukaci a sakaye sunan  sa sakamakon alaka da yake da ita da gidan man yace, ana tsaka da zuba man ne hukumomin gidan man suka hangi hukumar tsaro ta farin kaya dake yawo domin ganin an sayar da man yadda yake a farashin da gwamnati ta bayar, nan ne a kokarin su na gaggauta boyewa wutar ta tashi a motar.

Ba wannan ne karon farko da gobara ke tashi a gidajen man dake jihar kano ba sai dai a iya cewa wannan yazo da sauki domin kawo yanzu babu wani rahoton asarar rayuka sakamakon gobarar.

PRNigeria hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp