Sojojin Rundunar Operation Forest Sanity inda suka tarwatsa ‘yan bindiga 2 tare da tarwatsa maboyar su a karamar hukumar chikum dake jihar kaduna.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Wannan na kunshe ta cikin wata da kwamishinan tsaro da al’amarun ciki na jihar Kaduna Samuel Aruwa.
Wannan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da
Ta cikin wani rahoton bayan atisaye da Gwamnatin jihar ta samu ya bayyana cewa dakarun sun sami nasarar ne yayin wani bata kashi da sukayi Akan hanyar Kaboresha-Rijana dajin-Kuzo-Kujeni zuwa mashigar Gwanto zuwa Kachia.
Dakaru. Sun yi kwantan bauna akan hanyar Gwanto-Kwasau, inda su kuma ‘yan ta’addan suka nufi wajen haye bisa babura.
Sojojin sun sami natsara hallaka yan bindiga 2 tare da kwato babura 3.
Haka kuma dakarun sun sami nasarar tarwatsa maboyar dake kutura zuwa Rijana inda ‘yan Ta’addan suka afka cikin daji bayan sun hangi sojojin, inda aka sami babura 3 a wajen.
Haka kuma an sami damar kwato wasu abubuwan da suka hadar da kayan sojoji da wasu sauran kayayyakin yaki.
Gwamnatin jihar tace dakarun na cigaba da kai hare-haren kan ‘yan Ta’addan, ta bukaci Al’ummar jihar dasu cigaba da bada bayanan sirri.
PRNigeria hausa












