Shugaban Najeriya Muhammdu Buhari zai tafi ƙasar Senegal ranar Talata domin halartar taron ƙasa da ƙasa kan harkokin noma karo na biyu da za a gudanar a birnin Dakar.
Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar Femi Adesina ya fitar ranar Litinin.
Taron wanda shugaban Senegal kuma shugaban ƙungiyar ƙasashen Afirka ta AU, Macky Sall zai karɓi baƙunci – an shirya shi ne domin samar da kyakkyawan yanayin noma domin ciyar da haniyar Afirka.
Adesina ya ce maharta taron za su tattauna batun shigar da abinci da sauran kayan amfanin gona zuwa wasu ƙasashen, ciki har da Najeriya.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Ya ƙara da cewa yayin da nahiyar Afirka ke da mutum miliyan 249 da ke cikin ƙagin yunwa, taron – wanda shugabannin ƙasashen Afirka da ministocin kuɗaɗen da na noma na nahiyar, da ƙungiyoyin duniya za su halarta – zai saka aniyar kawar da yunwa a nahiyar Afirka nan da shekarar 2030.
Daga cikin tawagar da za ta yi wa shugaba Buhari rakiya zuwa taron har da ministan harkokin ƙasashen waje, Geoffrey Onyeama, da ministan noma da raya karkara, Dakta Mohammad Mahmood Abubakar, da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro Babagana Monguno da daraktan hukumar tattara bayanan sirri ta ƙasar Ambassada Ahmed Rufai Abubakar.












