Home General CBN ya kara Wa’adin kwanaki 10 kan karbar tsaffin kudi

CBN ya kara Wa’adin kwanaki 10 kan karbar tsaffin kudi

Babban bankin Najeriya CBN ya sanar da ƙara wa’adin daina karɓar tsofaffin kuɗi zuwa 10 ga watan Fabirairu.

Gwamnan babban bankin Godwin Emefiele ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.

Gwamnan ya ce ya zuwa yanzu CBN ya karɓi naira tiriliyan 1.9 na tsofaffin kuɗi, saura kuma naira biliyan 900 ya kammala karɓar tsofaffin kuɗaɗe.

Ya yi bayanin cewa sai da CBN ya nemi sahalewar Shugaba Muhammadu Buhari domin ɗage wa’adin karɓar tsofaffin kuɗin, wanda kuma ya amince a ƙara wa’adin da kwanaki 10.

“Sakamakon halin da ake ciki, mun nemi umarnin kuma mun samu daga shugaban ƙasa kamar haka: ƙarin kwanki 10 na karɓar tsofaffin kuɗi daga 31 ga watan Janairu zuwa 10 ga watan gobe na Fabirairu, za a ci gaba da karɓar kuɗin daga hannun ‘yan Najeriya a hukumance,” in ji sanarwar.

“Dama ta kwana bakwai, daga 10 zuwa 17 ga watan Fabrairu, domin al’umma su iya kai tsofaffin kudadensu Babban Bankin Najeriya bayan cikar wa’adi, kamar yadda doka ta 20(3) da ta 22 ta Babban Bankin ta tanada”.

“Bayanan da muka samu tun daga 2015, sun nuna kuɗaɗen da ke yawo a hannun ‘yan Najeriya sun kai naira tirliyan 1.4. Amma ya zuwa wata Oktoban 2022, alƙaluma sun nuna akwai sama da tirliyan 3.23 da ke yawo a hannu mutane.

“Wannan na nuna a naira biliyan 500 kacal a hannun bankuna, yayinda naira tirliyan 2.7 ke boye a hannun wasu ƙalilan.”

Gwamnan CBN ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su zama masu biyayya da haɗin kai wajen tabbatar an gama mayar da kuɗaɗen ba tare da wani tashin hankali ba.

Gabanin wannan mataki dai, da dama daga cikin ‘yan Najeriya sun fuskanci yanayi mara daɗi wajen mayar da tsofaffin kuɗaɗensu zuwa bankuna.

Cikin sanarwar gwamnan Babban Bankin ya yaba wa Shugaba Buhari na haɗin kai da ya bai wa CBN domin gabatar da wannan sauyin kuɗin wanda ya ce “ya kamata a riƙayi duk shekara 5 zuwa 8, amma Najeriya yanzu ta shafe shekara 19 ba ta sauya nata kuɗaɗen ba”.

PRNigeria hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp